2023: Yadda limamin Katolika ya fatattaki yan cocinsa da basu da katin zabe

2023: Yadda limamin Katolika ya fatattaki yan cocinsa da basu da katin zabe

  • Ga dukkan alamu, yan Najeriya musamman shugabannin addinai sun shirya ma wannan babban zabe na 2023 da ke zuwa
  • A karon farko, jagororin jama’a sun fara daukar batun yin katin zabe da muhimmanci duk a kokarinsu na son ganin mabiyansu sun fita zabe don kawo sauyi a kasar
  • A yanzu haka, wani limamin katolika ya hana mambobin cocinsa da basu da katin zabe shiga ciki don yin ibadah

Wani bidiyo ya bayyana kuma ya shahara a shafukan soshiyal midiya inda aka nuno wani limamin katolika yana umurtan mambobin cocinsa da basu da katin zabe da su koma gida.

Masu amfani da shafin twitter da dama sun wallafa bidiyon, ciki harda dan fafutukar siyasa, Rinu Oduala, wanda shine kan gaba wajen rijistan katin zabe.

2023: Yadda limamin Katolika ya fatattaki yan cocinsa da basu da katin zabe
2023: Yadda limamin Katolika ya fatattaki yan cocinsa da basu da katin zabe Hoto: @CCFNigeria
Asali: Twitter

Limamin Katolikan ya yi jawabi ga dandazon mabiyansa a gaban cocin, yana mai cewa kada wanda ya damu da zuwa coci cikinsu idan har basu da katin zabensu a hannu, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 50 da Bola Tinubu ya fito da su a siyasa har Duniya ta san da zamansu yau

Sai dai babu cikakken bayani kan wurin da abun ya faru ko kuma lokacin da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faston ya ce:

“Idan za ka zo ibadah, ka dauki katin zabenka, idan baka da katin zabenka a hannu, kada ma ka yi wahalar zuwa.
“Saboda babu amfanin samun kiristoci cike da coci, amma a lokacin zabe, yan tsirarunsu ne ke fita jefa kuri’a.
“Don haka, wannan na nufin adadinmu, yawanmu ba komai bane. Muna so kiristoci su dauki hakokinsu da muhimmanci sannan su sauke shi.”

Kalli bidiyon a kasa:

2023: CAN ta Aike Sako ga Masu Neman Shugabancin Kasa, Ta Sanar da Irin 'Dan Takarar da Zata Zaba

A wani labarin, kungiyar Kiristoci ta Kasa, CAN, ta ce duk jam'iyyar siyasa da ke son cin zaben shugabancin kasa a 2023 dole ne ta hada kai da coci.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya saki jerin sunayen jiga-jigan APC da wasu mutane da basa son Bola Tinubu

Samson Ayokunle, shugaban CAN, ya sanar da hakan a ranar Lahadi yayin jawabin bikin ranar damokaradiyya na 2022 wanda aka yi a Cibiyar Kiristoci ta Kasa da ke Abuja, The Cable ta ruwaito.

Ayokunle wanda ya samu wakilcin Wale-Oke, shugaban Pentecostal Fellowship of Nigeria, ya ce duk jam'iyyar da ke son samar da shugaban kasa na gaba dole ne ta hada kai da yankunan Kiristoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng