Ba sauran hamayya: Yahaya Bello ya ba da tallafi mai tsoka ga ci gaban kamfen din Tinubu

Ba sauran hamayya: Yahaya Bello ya ba da tallafi mai tsoka ga ci gaban kamfen din Tinubu

  • Bayan da Tinubu ya yi tattaki domin ganawa da Yahaya Bello, gwamnan ya yi kyauta mai tsoka ga fafutukar Tinubu
  • An ruwaito cewa, Yahaya Bello ya ba da kyauta ofishin zabe tare da bayyana goyon bayansa ga kokarin Tinubu
  • A baya dai an samu tashin kura tun bayan kammala zaben fidda gwanin shugaban kasa da Bello ya sha kaye a cikinsa

Abuja - Wani rahoton TSJ yace, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ba da gudummawar ofishi ga yakin neman zaben shugaban kasa na Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ziyarar da Tinubu ya kai masa a Abuja, Channels Tv ta ruwaito.

Da dama dai sun kagu domin sanin abin da aka tattauna tsakanin Yahaya Bello da Bola Ahmad Tinubu.

Kara karanta wannan

Manyan dalilai 4 da suka sa Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na APC

Ba hamayya: Yahaya Bello ya ba da tallafi mai tsoka ga ci gaban kamfen din Tinubu bayan shan kaye a zaben fidda gwani
Ba hamayya: Yahaya Bello ya ba da tallafi mai tsoka ga ci gaban kamfen din Tinubu | Hoto: naijanews.com
Asali: UGC

Tinubu ya isa wurin Bello ne tare da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, kamar yadda muka ruwaito muku a baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A martaninsa, Tinubu ya yaba da wannan karimcin kuma ya yi alkawarin yin aiki don hadin kan jam’iyya da kasa.

Ganawar dai wani bangare ne na sulhuntawa biyo bayan sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Bello na daya daga cikin ’yan takara da Tinubu ya doke su a takarar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Bello dai a baya ya bayyana akwai murda-murda a zaben fidda gwanin, lamarin da ya girgiza jama'ar Najeriya da dama a kafafen sada zumunta.

Sai dai, ana kyautata zaton ganawar Tinubu da Yahaya Bello ta yau din ta haifar da sakamako mai kyau da kuma da mai ido.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Bola Tinubu ya sa labule da gwamna Yahaya Bello

A tun farko, dan takarar shugaban ƙasa na APC kuma tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu, yanzu haka ya shiga taron sirri da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Masana siyasa na ganin hakan wani sashi ne a kokorin shawo kan fusatattun yan takarar da suka fafata da Tinubu a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Tinubu ya shiga taron ne tare da gwamnan Legas, Babajide Sanwo- Olu, gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, da kuma gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel