Yadda Aisha Buhari ta Fice Daga Taron APC a Fusace, Ta ki Raka Buhari Mika wa Tinubu Tuta

Yadda Aisha Buhari ta Fice Daga Taron APC a Fusace, Ta ki Raka Buhari Mika wa Tinubu Tuta

  • Rahotanni sun bayyana yadda Aisha Buhari ta fice daga taron APC a fusace bayan kammala jawabin Bola Ahmed Tinubu
  • An tattaro yadda aka dinga kiran Aisha Buhari ta raka Shugaba Buhari kan mimbari domin mika wa Tinubu tutar APC, amma ta ki
  • Bayan nan ta tashi a fusace ba tare da yi wa kowa sallama ba inda ta fice daga taron duk da ba a san silar fushin ta ba

Eagle Square, Abuja - Rahotanni daga filin wasa na Eagle Square da ke Abuja inda aka yi zaben fidda gwani na jam'iyyar APC, sun sanar da yadda Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa ta fice daga taron cikin matsanancin fushi.

Aminiya ta ruwaito cewa, Aisha Buhari ta figi motar ta inda ta yi ficewarta daga taron ranta bace, duk da kuwa an yi taron an tashi lami lafiya.

Kara karanta wannan

K'ayatattun Hotunan Shugaba Buhari yayin miƙa tuta ga ɗan takarar shugaban ƙasa a APC

Yadda Aisha Buhari ta Fice Daga Taron APC a Fusace, Ta ki Raka Buhari Mika wa Tinubu Tuta
Yadda Aisha Buhari ta Fice Daga Taron APC a Fusace, Ta ki Raka Buhari Mika wa Tinubu Tuta. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Aminiya tattaro yadda aka dinga kiran Aisha Buhari ta raka shugaban kasa Muhammadu Buhari kan mimbari amma ta yi biris.

Wannan lamarin ya faru ne bayan tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigon jam'iyyar APC na kasa ya kammala jawabin godiya bayan nasarar lashe zaben fidda gwanin da ya yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari kan mimbarin inda ya mika tutar jam'iyya ga Bola Tinubu a matsayin wanda zai nemi kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar a 2023.

Daga cikin wadanda suka raka Buhari zuwa kan mimbarin akwai, Sanata Abdullahi Adamu, Farfesa Yemi Osinbajo da Ahmad Lawan.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba a san musababin fushin uwargidan shugaban kasan ba a wurin taron.

Shugaban kasa Buhari ya mika turar takarar shuugaban kasa ga Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban kasa ya nemi ya jawo kwamacala a APC wajen fito da ‘Dan takaran 2023

A wani labari na daban, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya miƙa turar jam'iyyar APC ga Bola Ahmed Tinubu a wurin babban taro na zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa a Abuja.

Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta, Buhari Sallau, shi ne ya bayyana wannan cigaban tare da Hotuna a shafinsa na Twitter.

Shugaban tare da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da matar Osinbajo, ya damƙa tutar yayin rufe babban taron APC wanda ya tabbatar da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel