Da izinin Allah Kwankwaso ne zai zama shugaban kasa a 2023, in ji Shekarau

Da izinin Allah Kwankwaso ne zai zama shugaban kasa a 2023, in ji Shekarau

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya magantu a kan yadda sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 zai kasance
  • Shekarau ya nuna kwarin gwiwar cewa dan takarar jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa mai zuwa
  • Ya bayyana hakan ne a wurin babban taron jam’iyyar NNPP da ke gudana a babban birnin tarayya Abuja

Abuja - Jigon jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Da yake magana a wajen babban taron NNPP da ke guda a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a ranar Laraba, Shekarau ya ce yan Najeriya na fatan samun shugabanci mai ma’ana ne don haka Kwankwaso ne zai lashe zaben, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban kasa ya nemi ya jawo kwamacala a APC wajen fito da ‘Dan takaran 2023

Da izinin Allah Kwankwaso ne zai zama shugaban kasa a 2023, in ji Shekarau
Da izinin Allah Kwankwaso ne zai zama shugaban kasa a 2023, in ji Shekarau Hoto: Leadership
Asali: UGC

Shekarau, wanda ke wakiltan yankin Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, ya ce da izinin Allah Kwankwaso ne zai zama shugaban Najeriya a 2023.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yau babbar rana ce a tarihi. Ranar da za a dunga tunawa da ita. Mafarin wata tafiya ta shiga sabuwar kasa da muke mafarki, sabuwar kasa mai cike da buri.
“Babban shirinmu shine inganta rayuwar yan Najeriya. Yan Najeriya na ta jira, muna son chanja ci gaban, sauya ci gaban da gaskiya, chanja rayuwar matasa zuwa mai inganci.
“Muna son kawo shugabanci da zai sa duk yan kasa su ga cewa suna da muhimmanci. Babban taron NNPP yana da nasara saboda Kwankwaso ne zai zama shugaban kasa a 2023 da izinin Allah.”

Da yake magana a taron, Shugaban NNPP na kasa, Rufa’i Alkali, ya bayyana cewa suna da maza da mata masu mutunci da Za su cike gurbin shugabanci a kasar nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan hanyar da za a bi wajen zabar dan takarar APC

Kwankwaso Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar NNPP

A gefe guda, mun ji cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka yi a ranar Laraba.

Kwankwaso ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasar na NNPP ne bayan daligets daga jihohi sun sahale masa da baki kamar yadda The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel