Yanzu-Yanzu: Kwankwaso Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar NNPP

Yanzu-Yanzu: Kwankwaso Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar NNPP

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Kano ya zama dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam'iyyar NNPP a zaben 2023
  • An zabi Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban kasar ne yayin gangamin jam'iyyar da aka yi a Abuja inda daligets 774 daga jihohi 36 suka amince masa
  • Ana fatan Kwankwason zai fafata da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki da wasu yan takarar daga jam'iyyu a kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka yi a ranar Laraba, Sahara Reporters ta rahoto.

A halin yanzu jam'iyyar NNPP tana gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasar ta a filin Moshood Abiola Stadium da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Gwamna ya dakatar ASUU a jiharsa, ya umarci Malaman jami'o'i su koma aiki ko ya ɗau mataki

Yanzu-Yanzu: Kwankwaso Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Shugaban Kasa Na NNPP
Kwankwaso Ya Zama Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar NNPP. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamkwaso ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasar na NNPP ne bayan daligets 774 daga jihohi 36 sun sahale masa da baki kamar yadda The Punch ta rahoto.

Idan za a iya tunawa, shugaban jam'iyyar na NNPP na kasa, Boniface Aniegbonam, ya ce Kwankwaso shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a shekarar 2023 a yayin taron manema labarai a Legas a ranar Juma'a da ta gabata.

Kwankwaso shine gwamnan Jihar Kano daga shekarar 1999 zuwa 2003 sannan ya sake yin gwamna daga 2011 zuwa 2015.

Bayan ya fadi zabe a 2003, an nada shi Ministan Tsaro a Jamhuriya ta hudu duk da cewa ba shi da wani horaswa na aikin soja daga 2003 zuwa 2007, a karkashin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Daga bisani an zabe shi sanata a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai wakiltar Kano Central a majlisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel