Yan Takarar Shugaban Kasa A APC Su 7 Sun Ki Yarda Da Sunayen Mutum 5 Da Gwamnoni Suka Mika Wa Buhari

Yan Takarar Shugaban Kasa A APC Su 7 Sun Ki Yarda Da Sunayen Mutum 5 Da Gwamnoni Suka Mika Wa Buhari

  • Masu neman karara shugaban kasa a jam'iyyar APC su bakwai sun nuna jin amincewarsu da sunayen yan takara 5 da gwamnoni suka mika wa Shugaba Buhari
  • Yan takarar bakwai cikin wata sanarwa Ogbonnaya Onu ya fitar a madadinsu sun zargi gwamnonin da yunkurin kawo cikas ga sasanci da Buhari ya umurci yan takarar su yi
  • Sanarwar ta ce magoya bayansu da sauran al'umma su yi watsi da batun yan takarar 5 domin ba daga bakin shugaban jam'iyya Abdullahi Adamu aka ji ba kuma su ba a tuntube su ballantana a yi wani sasanci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Wasu daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a APC sun yi watsi da sunayen yan takar da gwamnoni suka mika wa Shugaba Buhari don ya zabi magajinsa daga cikinsu, rahoton Tribune.

Wadanda ba su yarda da hakan ba akwai Gwamnan Cross Rivers Ben Ayade; Tsohon Karamin Ministan Ilimi, Emek Nwajiubu; Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, Tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha da dan kasuwa Tein Jack-Rich.

Yanzu: Yan Takarar APC 7 Sun Ki Yarda Da Sunayen Mutum 5 Da Gwamnoni Suka Mika Wa Buhari
Yan Takarar Shugaban Kasa Na APC 7 Sun Ki Yarda Da Sunayen Mutum 5 Da Gwamnoni Suka Mika Wa Buhari. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong ne ya tabbatar da jerin sunayen.

Ba mu san da zancen mika wa Buhari sunan yan takara 5 ba don ya zabi magaji

Sai dai, wata sanawar a madadin yan takarar bakwai da Onu ya fitar a ranar Talata, yan takarar bakwai sun ce matakin na gwamnonin arewa wasa ne ya wuce gona da iri.

"Cikin awanni da suka wuce, magoya bayanmu suna ta kiran game da jerin sunayen mutum biyar da aka mika wa Shugaba Buhari ya zaba magajinsa.

"Iya saninmu, ba a bawa shugaban kasa wasu sunaye ba, abin da gwamnonin suka yi wasa ce ta wuce gona da iri da nufin wasa da hankalin yan Najeriya musamman mu yan kudu.
"Abin da shugaban kasa ya ce shine dukkan yan takara har da yan arwa su hadu su fitar da mutum daya. A yanzu, ba a gayyace mu wani taro inda aka amince da sunayen da za a bawa shugaban kasa ba.
"A cikin jerin sunayen, mutum daya ne kawai daga kudu maso gabas kuma muna maganan yi wa kudu adalci. Abin da gwamnonin suka yi wasan kwaikwayo ne kawai. Kuma wannan gwamnonin ke maganan daidaito da adalci amma suka ware kudu maso gabas.
"Tunda ba a yi sasanci ba, babu wani sunaye da aka bawa shugaban kasa, abin da suka yi wasa ne kuma ba za su yi nasara ba.
"Muna da masaniya cewa an yi wa wadannan gwamnonin alkawarin wasu abubuwa don su lalata lamarin saboda dan takara daya ya samu nasara amma ba za su yi nasara ba," in ji sanawar.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan takaran sun kuma ce Abdullahi Adamu ne shugaban APC kuma duk wani mataki da masu ruwa da tsaki suka dauka shine zai sanar idan ba haka ba abin bai da tushe.

Daga karshe sun yi kira ga yan Najeriya su yi watsi da sanarwar suna mai cewa kawo yanzu babu wani sasanci da aka yi

Gwamnonin APC Na Arewa Sun Goyi Bayan Mulki Ya Koma Kudu, Sun Buƙaci Ƴan Takara Daga Arewa Su Janye

A wani rahoton, kun ji gwamnonin jihohin arewa na jam'iyyar APC sun nuna goyon bayansu ga zaben dan kudu a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar takarar shugaban kasa a 2023.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar bayan wani taro da suka yi a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel