El-Rufai: Dalilin da yasa Yahaya Bello ya fice a taron Buhari da gwamnonin APC na Arewa

El-Rufai: Dalilin da yasa Yahaya Bello ya fice a taron Buhari da gwamnonin APC na Arewa

  • Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana gaskiyar dalilin da yasa gwamnan jihar Kogi ya fice daga ganawar Buhari da gwamnonin APC na Arewa
  • El-Rufai ya ce, akwai abin da gwamnan bai amince dashi ba, wanda hakan yasa ya fice daga ganawar tasu
  • Matsala ta fara samuwa ne a APC tun lokacin da gwamnonin suka dage cewa dole a mika tikitin takara Kudu

Abuja - Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce Yahaya Bello, gwamnan Kogi, ya fita daga taron gwamnonin jam’iyyar APC na Arewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda uzuri.

El-Rufai ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin bayan gwamnonin sun kammala ganawarsu da Buhari, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kowa ya bi: An sake samun Gwamnan Arewa da ke goyon bayan ‘Yan kudu su karbe mulki

Abin da yasa gwamnan Kogi ya fice daga taron gwamnoni
El-Rufai: Dalilin da yasa Yahaya Bello ya fice a taron Buhari da gwamnonin APC na Arewa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai, El-Rufai ya ce gwamnoni 13 daga cikin 19 na APC daga Arewa sun amince da cewa a mika tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar zuwa Kudu.

Gwamnan na Kaduna, ya ce Bello, wanda dan takarar shugaban kasa ne na APC, ya yanke shawarar kin halartar taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar El-Rufai, gwamnan jihar Kogi ya ki amincewa da matakin da takwarorinsa suka dauka na mika tikitin takarar shugaban kasa a Kudu, inji Daily Post.

A kalamansa:

"Gwamnan jihar Kogi ya zabi ya fita daga ganawa da shugaban kasa saboda yasan cewa bai amince da matsayarmu ba.
“Akwai gwamnonin APC 14 a cikin jihohin Arewa 19. Mu 13 muna kan wannan batu a shafi daya kuma duk mun zo ganin shugaban kasa. Amma gwamnan jihar Kogi ya ba da uzuri, kuma yana cikin ‘yancinsa na dimokuradiyya ya ba uzuri.”

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa a APC: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya bar taron gwamnonin APC a fusace

Sai dai, a nasa jawabin, shugaban kungiyar gwamnonin PGF, Atiku Bagudu, ya ce zai kawo zaman lafiya a kai tikitin takarar shugaban kasa a Kudu.

Shugaban APC ya fusata, ya fatattaki 'yan jarida a sakateriyar APC

A wani labarin, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya fatattaki ‘yan jarida da aka amince da su da ke daukar labaran jam’iyyar daga sakatariyar ta na kasa da ke Abuja rahoton Leadership.

Daya daga cikin jami’an tsaro a sakatariyar, wanda ya mika bayanan ga manema labarai tare da neman su fice daga harabar sakatariyar jam’iyyar, ya ce suna aiki ne da umarnin shugaban jam’iyyar na kasa.

Ya ce Adamu ya ce su fitar da ‘yan jarida daga sakatariyar a kan cewa zai dawo sakatariyar ne domin yin taro, kuma wurin ya cika makil.

Asali: Legit.ng

Online view pixel