Da duminsa: Buhari da Gwamna Yahaya Bello sun saka labule a Aso Rock

Da duminsa: Buhari da Gwamna Yahaya Bello sun saka labule a Aso Rock

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya labule da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi kuma 'dan takarar shugabancin kasa
  • Gwamna Yahaya Bello ya barranta kansa da hukuncin gwamnonin arewa na APC da suka ce a mika mulki hannun 'dan kudu
  • Masu hasashe na ganin cewa, Buhari da Bello suna zantawa ne kan batun ya janye ko kuma ya cigaba da neman takarar

Aso Rock, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a halin yanzu ya sanya labule inda yake ganawa da gwamnan jihar Kogi kuma 'dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar APC, Yahaya Bello, a fadar Aso Rock da ke Abuja.

Gwamnan jihar Kogin yana daya daga cikin 'yan takara 23 da ke fatan yin caraf da tikitin takarar shugabancin kasa a APC a zaben 2023 mai gabatowa, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Rikici a APC yayin da ake yunkurin magudi a jerin sunayen deliget

Da duminsa: Buhari da Gwamna Yahaya Bello sun saka labule a Aso Rock
Da duminsa: Buhari da Gwamna Yahaya Bello sun saka labule a Aso Rock
Asali: Original

Duk da gwamnonin APC daga arewa sun yanke shawara kan mika mulki kudu, Gwamna Bello ya barranta kansa daga wannan hukuncin.

Har a halin yanzu, ba a san me Bello da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke tattaunawa ba, amma akwai hasashen da ke bayyana cewa ta yuwu suna tattaunawa ne kan yadda zai janye ko a'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel