Taron APC: Har yanzu Buhari bai zartar da hukunci kan mika mulki kudu ba - Badaru

Taron APC: Har yanzu Buhari bai zartar da hukunci kan mika mulki kudu ba - Badaru

  • Daya daga cikin masu takarar kujerar shugaban kasa a APC, Gwamna Abubakar Badaru, ya ce har yanzu Shugaba Buhari bai yanke shawara kan mika mulki kudu ba
  • Ya ce gwamnonin arewa 11 dai sun bashi shawara ne kan cewa ya kamata a mika mulki kudu duba ga yanayin da ake ciki, inda suke sa ran zai dauki shawarar tasu
  • Sai dai ya ce su za su kasance masu biyayya ga duk matakin karshe da shugaban kasar ya zartar kan wanda zai gaje shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ya bayyana cewa har yanzu gwamnonin arewa suna sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi aiki da shawarar da suka bayar na mika mulki zuwa yankin kudu.

Badaru ya fadi hakan ne yayin wata hira da sashin Hausa na BBC a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Zaben Fidda Gwani: Matasan Kano Sun Balle Zanga-Zanga kan Hukuncin Gwamnonin APC

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shugabannin jam’iyyar a arewa sun goyi bayan mika mulki zuwa yankin kudancin kasar a ranar Asabar da ta gabata.

Taron APC: Har yanzu Buhari bai zartar da hukunci kan mika mulki kudu ba - Badaru
Taron APC: Har yanzu Buhari bai zartar da hukunci kan mika mulki kudu ba - Badaru Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mista Badaru, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar, ya ce har yanzu Buhari bai riga ya zartar da hukunci kan lamarin ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yi bayanin cewa jawabin gwamnonin jam’iyyar 11 kan batun mika mulkin shawara ce kawai amma ba wai an ayyana bane, rahoton Premium Times.

Ya ce:

“Na yi mamaki da jin cewa wai an kulla wata yarjejeniya da sa hannun mutane, wanda a zahirin gaskiya shawara ce da ake sa ran Baba (Buhari) zai dauka. Idan ya amince da shi, za a aiwatar da shi kuma idan bai amince ba, za mu ci gaba da kowace shawara ya gabatar tunda dukkaninmu gwanonin arewa masu biyayya ne ga Buhari kuma duk abun da ya ce, da izinin Allah za mu aikata shi.”

Kara karanta wannan

Buhari ya amince zai marawa Tinubu baya don ya zama shugaban kasa – Buba Galadima

Ya bayyana cewa gwamnonin arewa sun zabi Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Gwamna Simon Lalong na Filato da Abdullahi Sule na Nasarawa domin su gana da shugaban kasar kan bukatar.

Ya ci gaba da cewa:

“Da gaske ne, gwamnonin arewa, kimanin su 11, harda ni ciki, mun tattauna lamura sannan mun duba yanayin. Mun yanke hukuncin shawartan Buhari cewa duba ga lamarin, zai fi a mika shugabanci kudu.
“Idan shi (Buhari) ya yarda da shi, za a aiwatar da shi. Sabanin haka, idan yana da shawarar da ta fi wannan, sai ya bamu a matsayinsa na ubanmu, mu kuma a matsayinmu na yaransa.
“Bana a hurumin janyewa har sai na ji abun da Buhari ya ce. Idan ya ce mu ci gaba da takara, za mu ci gaba. Idan ya ce mu janye sannan mu marawa kudu baya, za mu aikata haka sannan mu lallashi sauran mutane daga arewa su hakura da takararsu saboda Baba ya ce mulki ya koma kudu. Sai dai idan Baba ya ce mu ci gaba, za mu ci gaba.”

Kara karanta wannan

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

Da wannan ci gaban, haka na nufin har yanzu yan takara 23 ne a tseren neman tikitin jam’iyyar.

‘Ko dan arewa ko ta bare' Matasan APC sun caccaki gwamnonin arewa kan kai tikitin magajin Buhari kudu

A gefe guda, wata gamayyar kungiyoyin matasan arewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yi watsi da hukuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin arewa 11 na mika mulki ga yankin kudancin kasar.

Kungiyoyin matasan na ‘APC Progressives Youth Elements da North-East Youth Forum of APC’ wadanda suka gudanar da zanga-zanga a garin Bauchi a ranar Lahadi, sun bayyana cewa gwamnonin sun nuna son zuciya tunda har suka yarda a mika mulki kudu.

Sun kasance dauke da kwalaye da rubuce-rubuce kamar: “Ba ma goyon bayan mika mulki zuwa kudu”, “Ba za mu yarda da hukuncin gwamnoni goma sha daya ba, “Saboda son zuciyarsu ne.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel