‘Ko dan arewa ko ta bare' Matasan APC sun caccaki gwamnonin arewa kan kai tikitin magajin Buhari kudu

‘Ko dan arewa ko ta bare' Matasan APC sun caccaki gwamnonin arewa kan kai tikitin magajin Buhari kudu

  • Kungiyoyin matasan jam'iyyar APC a arewa sun nuna bore a kan shirin mika shugabancin kasar ga yankin kudancin kasar
  • Matasan sun ce sam basu yarda da wannan yunkuri na gwamnonin yankin 11 ba, inda suka ce lallai dan arewa suke so a tsayar
  • Hakazalika sun zargi gwamnonin arewa da kwadayin kujerar mataimakin shugaban kasa, wanda a cewarsu wannan dalilin ne yasa suka yarda da tsarin

Bauchi - Wata gamayyar kungiyoyin matasan arewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yi watsi da hukuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin arewa 11 na mika mulki ga yankin kudancin kasar.

Kungiyoyin matasan na ‘APC Progressives Youth Elements da North-East Youth Forum of APC’ wadanda suka gudanar da zanga-zanga a garin Bauchi a ranar Lahadi, sun bayyana cewa gwamnonin sun nuna son zuciya tunda har suka yarda a mika mulki kudu.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai, Zulum da sauran gwamnonin arewa masu goyon bayan kudu maciya amana ne – Kungiyar arewa

Sun kasance dauke da kwalaye da rubuce-rubuce kamar: “Ba ma goyon bayan mika mulki zuwa kudu”, “Ba za mu yarda da hukuncin gwamnoni goma sha daya ba, “Saboda son zuciyarsu ne.”

‘Ko dan arewa ko ta bare' Matasan APC sun caccaki gwamnonin arewa kan kai tikitin magajin Buhari kudu
‘Ko dan arewa ko ta bare' Matasan APC sun caccaki gwamnonin arewa kan kai tikitin magajin Buhari kudu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Da yake magana da yawun daya daga cikin kungiyoyin, shugaban matasan APC, Alamin Bala Mai’auduga, ya bayyana cewa lokaci bai yi ba da kudu za ta shugabanci kasar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Mun yi Allah wadai da matakin gwamnonin arewa 11 da suka goyi bayan kudancin kasar.
“Mu matasan arewa bama ganin lokaci ya yi da wani dan kudu zai karbi shugabanci.
“Abun da gwamnonin suka yi don son zuciyarsu ne. mu matasan arewa, wadanda mune kimanin kaso 70 cikin 100 na al’ummar kasar nan, mun ce a’a.
“Muna kira ga shugabanmu na kasa, Abdullahi Adamu, da ya shigo cikin wannan lamari sannan ya samar da mafita mai dorewa a kan haka.

Kara karanta wannan

Rikici: Zai zama bala'i idan APC ta hana Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, Shettima

“Ba za mu marawa kowani dan takara na kudu baya ba. Wadannan gwamnoni 11 da suka zartar da hukunci ba su kadai ne mutane a arewa ba.
“Suna aikata haka ne don son zuciyarsu.”

Daily Post ta kuma rahoto cewa, a nasa bangaren, shugaban kungiyar matasan APC, Ibrahim Hashim Abdullahi, ya yi zargin cewa gwamnonin sun yarda da wannan shawarar ne don daya daga cikinsu ya amfana daga nada shi a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Ya yi ikirarin cewa da yunwa, rashin tsaro, talauci da ke yankin, akwai bukatar a ci gaba da rike mulki don samun ci gaba.

“Ba za mu marawa kowani dan takara daga kudu baya ba, sai dan arewa. An bar mu a baya sosai.”

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

A yau Litinin, 6 ga watan Yunin 2022 ne jam'iyyar APC ta ke gudanar da zaben fitar da gwani cikin 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Hotuna: 'Yan a mutun Jonathan sun mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikiti

Daga cikin 'yan takara, duk wanda ya lashe zaben yau shi ne zai samu tikitin fitowa takarar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa a karkashin jam'iyyar mai mulki.

Akwai 'yan takara har 22 da deliget 2322 daga jihohi 36 na kasar nan za su zaba, wanda hakan ne zai bayyana makomar 'yan takarar bayan kammalar zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel