Buhari ya amince zai marawa Tinubu baya don ya zama shugaban kasa – Buba Galadima

Buhari ya amince zai marawa Tinubu baya don ya zama shugaban kasa – Buba Galadima

  • Injiniya Buba Galadima ya jadadda cewa akwai yarjejeniyar fahimta tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Bola Tinubu cewa zai mara masa baya don ya gaje shi a 2013
  • Galadima ya bayyana cewa alkawari ne aka daukarwa Tinubu cewa idan har ya samawa Buhari goyon bayan da yake bukata toh shima za a saka masa idan ya gama wa'adinsa
  • Ya ce an yarda da haka ne a lokacin da kokarin tsayar da babban jagoran na APC a matsayin mataimakin shugaban kasa bai yiwu ba saboda tikitin zama na Musulmi-Musulmi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya tabbatar da cewar akwai yarjejeniya tsakanin shugaban kasar da tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Tinubu, cewa zai marawa kudirinsa na son zama shugaban kasa baya.

Galadima ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da jaridar Punch gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Majiyar Cikin Gida Ta Fallasa Sunan 'Dan Takarar da Buhari ya Karkata Hankali Wurinsa

Buhari ya amince zai marawa Tinubu baya don ya zama shugaban kasa – Buba Galadima
Buhari ya amince zai marawa Tinubu baya don ya zama shugaban kasa – Buba Galadima Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sai dai kuma, Galadima ya ce ko shakka babu shugaban kasar zai tsayar da dan takarar da yake so ne a yayin zaben fidda gwanin jam’iyyar ta APC.

Buba ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ba ka bukatar ka zama boka ko mallam kafin ka san cewa shugaban kasar zai tursasa duk wanda yake so ya zama dan takarar APC. Amma abun da ya kamata mutum ya duba shine ko zai aikata hakan da tunani, tare da la’akari da ra’ayoyin mafi yawan mambobin jam’iyyarsa. Amsata ita ce a’a. don haka, duk wanda ya tursasa zai haddasa cece-kuce, fadace-fadece da ayyukan da suka saba jam’iyya sosai. Wannan zai kawowa APC cikas."

Game da ko an kulla yarjejeniya a wani lokaci cewa Tinubu zai gaji Buhari, Galadima ya ce:

“Ba wai yarjejeniya aka kulla kai tsaye ba, amma akwai fahimta saboda Tinubu da wani mutum da shugaban kasa da kuma wani mutum sun zauna sannan bayanin da muka samu shine cewa sun yarda cewa idan Tinubu ya taimaki Buhari ya lashe zabe, zai zama mataimakin shugaban kasa. Lokacin da hakan bai yiwu ba, sai suka kira shi suka bukaci ya taimaka saboda abubuwan da suka faru a lokacin, wanda ba zai ba da damar tikitin musulmi da musulmi ba.

Kara karanta wannan

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

“Sai suka ce duk abun da yayi, ya tabbatar da ganin cewa Buhari ya zama shugaban kasa sannan cewa shi (Buhari) shima zai yi duk mai yiwuwa don taimakawa Tinubu ya zama shugaban kasa. Alamu sun nuna yanzu suna janyewa daga wannan fahimtar. Kuma alkawari, alkawari ne ko a rubuce ko ba a rubuce ba saboda idan za ka iya juyar da shi, Allah ya san zuciyarka. Kuma Allah ba Ya karbar cin amana. Idan aka yi alkawari, ko mai tsami ne ko mai daci, ko mai dadi, sai ka hadiye shi.
“Yanzu, kamar suna son janye wannan fahimtar da Tinubu. Wannan ne dalilin da yasa Tinubu ya cika da dacin rai kuma na fahimci wannan bakin cikin, saboda abun da ya same shi, wanda na fada masa a shekarun baya. Na fada masa abun da zai faru da shi. Kuma duk abun da nayi hasashe a shekaru baya gasu suna faruwa a yanzu. Addu’ata gare shi (Tinubu) ita ce Allah yasa ya fita daga wannan lamarin cikin koshin lafiya ba tare da abu ya same shi ba. Wannan ita ce babbar addu’ata gare shi.

Kara karanta wannan

Manyan matsaloli 4 da ke gaban APC yayin da zaben fidda gwani ya gabato

"Amma a gare shi, kamar an riga an yi masa juyin mulki. Hanya daya da zai iya samun karfinsa ita ce idan jam’iyyar ta amince ta yi zaben fidda gwani. Idan jam’iyyar ta amince ta yi zaben fidda gwani, ba na tantama a raina cewa Tinubu zai iya yin nasara, amma dangane da matsayar da suke son dauka, ya fita daga wasan.”

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

A yau Litinin, 6 ga watan Yunin 2022 ne jam'iyyar APC ta ke gudanar da zaben fitar da gwani cikin 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar.

Daga cikin 'yan takara, duk wanda ya lashe zaben yau shi ne zai samu tikitin fitowa takarar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa a karkashin jam'iyyar mai mulki.

Akwai 'yan takara har 22 da deliget 2322 daga jihohi 36 na kasar nan za su zaba, wanda hakan ne zai bayyana makomar 'yan takarar bayan kammalar zaben.

Kara karanta wannan

2023: Muhimman dalilai 3 da za su iya sa Tinubu ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel