Abin da yan takara suka faɗa wa Buhari game da wanda zai zaɓa ya gaje shi a 2023

Abin da yan takara suka faɗa wa Buhari game da wanda zai zaɓa ya gaje shi a 2023

  • Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce a wurin ganawarsu da shugaba Buhari sun amince su koma bayan duk wanda ya zaɓa
  • Gwamnan ya ce jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu na wurin taron kuma bai musa kan matsayar ba, don haka ya amince
  • Ya ce matsayar da gwanonin arewa suka cimma kan kai takara kudu ra'ayin su ne kawai, ba shi da alaƙa da yan Najeriya

Abuja - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya ce yan takarar shugaban ƙasa na APC sun amince su goyi bayan duk wanda Shugaba Buhari ya zaɓa ya gaje shi.

A ranar Asabar, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da baki ɗaya yan takara a fadarsa Aso Villa da ke babban birnin tarayya Abuja.

A taron Buhari ya bukace su da su yi maslaha a tsakanin su, su fitar da ɗan takara guda kafin ranar zaɓen fidda gwani, kamar yadɗa The Cable ta ruwaito.

Gwamna Yahaya Bello na Kogi.
Abin da yan takara suka faɗa wa Buhari game da wanda zai zaɓa ya gaje shi a 2023 Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Gwamana Yahaya Bello, ɗaya daga cikin masu hangen kujerar ta shugaban ƙasa, ya ce a shirye yake ya koma bayan wanda Buhari ya zaɓa daga cikin su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta ruwaito Bello ya ce:

"Duk wanda shugaban ƙasa ya fito da shi, zan goyi bayansa 100 bisa 100, ba ni kaɗai ba, a liyafar da muka ci tare, kusan kashi ɗari, zan iya cewa dukkan mu mun amince duk wanda Buhari ya zaɓa zamu mara masa baya."

Yayin da aka tambaye shi ko Bola Ahmed Tinubu, ya na cikin waɗan da suka amince da haka, Bello ya ce ya halarci taron kuma bai musa ba.

"Yana wurin a zaune kuma bai musa da abun ba, saboda haka idan wani ya yi magana a madadinka kuma baka da wani abu da ya saɓa wa haka, sannan ka yi shiru, hakan na nufin ka yarda."

Matsayar gwamnonin arewa ba ta shafe mu ba - Bello

Bugu da ƙari, Bello ya ce matsayar da gwamnonin arewa suka cimma na kai tikitin takara kudu bai shafe su ba kwata-kwata. Ya kira matakin da, "Ra'ayin kai da kai."

"Matsayar da takwarorina suka ɗauka ra'ayin kan su ne, bai shafi yan Najeriya ba, kuma bai shafe ni ba bare jam'iyya saboda gwamnonin arewa kaɗai ba su ne gangar APC ba."

A wani labarin kuma Ganduje ya ce yawan sauya sheƙar Kwankwaso da Shekarau zai shafe su a babban zaɓen 2023

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana haɗuwar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau da '' tsilla-tsillan siyasa.''

Ganduje ya ce tsalle-tsallen yan siyasan biyu daga nan zuwa can zai sa ba zasu iya kai labari ba, APC zata cigaba da jan zarenta a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel