Kwankwaso da Shekarau ba zasu kai labari ba a 2023 saboda tsilla-tsilla, Ganduje

Kwankwaso da Shekarau ba zasu kai labari ba a 2023 saboda tsilla-tsilla, Ganduje

  • Gwamna Ganduje na jahar Kano ya ce yawan sauya shekar Sanata Shekarau da Kwankwaso, ya rage musu ɗumbin magoya baya
  • Ganduje ya ce tsalle-tsallen yan siyasan biyu daga nan zuwa can zai sa ba zasu iya kai labari ba, APC zata cigaba da jan zarenta a Kano
  • A cewarsa halin da APC ta tsinci kanta a jihar da ficewar mambobinta ba zai hana ta samun nasara ba a zaɓen da ke tafe

Kano - Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana haɗuwar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau da ''tsilla-tsillan siyasa.''

Idan baku manta ba, a baya-bayan nan ne tsohon gwamnan Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya sauya sheƙa da ga jam'iyyar APC zuwa NNPP mai kayan marmari.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan Oyo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Daily Trust ta rahoto cewa hakan ta sa Shekarau ya haɗa inuwa ɗaya da magajinsa kuma wanda ya gada, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda tun farko ya bar PDP zuwa NNPP.

Gwamnan Kano, Dakta Ganduje.
Kwankwaso da Shekarau ba zasu kai labari ba a 2023 saboda tsilla-tsilla, Ganduje Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Amma da yake jawabi yayin ziyarar yan jaridar TVC, Ganduje ya ce jam'iyyar APC ke kan gaba wajen damar cigaba da mulkin Kano duk da kalubalen sauya sheka da ya addabeta a kwanan nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce tun da Kwankwaso da Shekarau suka fara sauye-sauyen sheƙa a 2014, daga nan suka fara rasa mabiya a duk tsalle ɗaya da suka yi na canza sheka.

Shin APC zata kai labari a Kano?

A cewar gwamna Ganduje, Khadimul Islam, haɗuwar manyan yan siyasan biyu ba zai cutar da APC ko Najeriya ba ko kaɗan.

A kalamansa, gwamna Ganduje ya ce:

Kara karanta wannan

Matakai 3 da Tinubu zai iya dauka idan bai samu tikitin shugaban kasa na APC ba

"Tsofaffin gwamnonin biyu yan siyasa ne ma su amfani ba ni da tantama a kan haka, amma a siyasa idan kana yawan canza jam'iyya, zaka rasa masoya ne a wasu matakai."
"Muna tare da Kwankwaso a PDP sai muka sauya sheka zuwa APC kuma muka rasa wasu magoya baya, bayan haka shi ya sake komawa PDP, nan ma ya rasa masoya, ya koma NNPP kuma hakan ta sake faruwa. Haka shi ma Shekarau."
"Saboda haka idan mutum na yawan canza wurin zama a siyasar yanzu, magoya bayansa zasu ke raguwa. Ina ganin APC ta gama shirin lashe zaɓe duba da haɗuwar su biyu a wuri ɗaya."

A wani labarin kuma Jam'iyyar PRP ta sanar da sakamakon zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023

Jam'iyyar Peoples Redemption Party wato PRP ta sanar da sakamakon fidda gwani na takarar shugaban ƙasa wanda ya gudana ranar Lahadi.

Zaɓen, wanda ya gudana a babbar Sakatariyar PRP ta ƙasa da ke Abuja, ya nuna cewa Kola Abiola, shi ne ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023.

Kara karanta wannan

APC ta gamu da babban cikas, Ɗan takarar gwamna da dubbannin magoya baya sun fice daga jam'iyyar

Asali: Legit.ng

Online view pixel