Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu ibada

Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu ibada

  • Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa masu ibada a cocin katolika na St Francis a garin Owo da ke jihar Ondo
  • Buhari ya ce makiya ne suka aikata ta'asar, yana mai cewa za su fuskanci bakin cikin duniya da na lahira
  • Ya kuma yi gaje ga iyalan wadanda abun ya ritsa da su da kuma gwamnatin jihar Ondo inda ya bukaci hukumar bayar da agaji ta kai dauki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin yan bindiga a kan cocin katolika na St Francis da ke Owo, hedkwatar karamar hukumar Owo ta jihar Ondo, yana mai cewa duhu ba zai taba shafe haske ba, Channels tv ta rahoto.

Wasu tsagerun yan ta’adda ne suka tayar da cocin a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, inda suka kashe masu ibada da dama sannan wasu da yawa sun jikkata.

Kara karanta wannan

Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani

Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu bauta
Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu bauta Hoto: Channels tv
Asali: UGC

Awanni bayan faruwar lamarin, Buhari ya yi martani inda ya ce Najeriya ba za ta taba mika wuya ga wadanda ya bayyana a matsayin mugayen mutane ba.

Shugaban kasar a cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara kan harkokin labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa makiya ne kawai za su aikata wannan mummunan aikin, yana mai cewa za su fuskanci bakin cikin duniya da na lahira.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buhari ya kuma jajanta wa iyalan wadanda aka kashe a cocin da gwamnatin jihar Ondo, inda ya bukaci hukumomin agajin gaggawa da su kai dauki ga wadanda suka jikkata.

Ya ce:

“Duk rintsi duk wuya, kasar nan ba za ta taba mika wuya ga miyagu da mugayen mutane ba, kuma duhu ba zai taba yin nasara a kan haske ba. Najeriya za ta yi nasara a karshe."

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutane da dama sun mutu yayin da bam ya tashi a cocin Katolika da ke Ondo

Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani

A gefe guda, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce gwamnatinsa za ta kamo wadanda suka kai hari kan wani coci a karamar hukumar Owo ta jihar, jaridar The Cable ta rahoto.

A yau Lahadi, 5 ga watan Yuni ne wasu yan bindiga suka farmaki cocin katolika na St Francis yayin da ake shirin tashi. An tattaro cewa mutane da dama sun mutu a harin ciki harda yara da mata.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin mugunta da shaidanci, ya kuma ce hakan cin zarafi ne ga mutanen Owo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel