Babban Dan Takarar Shugaban Kasa na PDP Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Sha Kaye a Zaben Fidda Gwani na 2023

Babban Dan Takarar Shugaban Kasa na PDP Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Sha Kaye a Zaben Fidda Gwani na 2023

  • Mai neman takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2023, Dele Momodu ya bayyana dalilin da yasa ya sha kaye a zaben fidda gwani
  • Momodu ya kuma zargi shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, daga kudu da yi wa junansu zagon kasa
  • A cewar Momodu, an yi wa Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers taron dangi kuma ya san hakan tun kafin zaben fidda gwanin na ranar Asabar

Daya daga cikin manyan yan jarida wanda ya yi takara a zaben fidda gwani na kujerar shugabancin kasa ta PDP ta 2023 a ranar Asabar 28 ga watan Mayu, ya yi bayanin dalilin da yasa ya fadi zaben.

Dele Momodu, yayin hira da aka yi da shi a TVC News ya ce manyan shugabannin PDP daga kudancin kasar sun gaza hada kansu wuri guda duk da kiraye-kiraye da ake yi na neman ganin an shugaban kasa daga yankinsu.

Kara karanta wannan

Na Yi Matuƙar Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP

Babban Dan Takarar Shugaban Kasa na PDP Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Sha Kaye a Zaben Fidda Gwani na 2023
Dan Takarar Shugaban Kasa na PDP Ya Fadi Dalilin Da Yasa Ya Sha Kaye a Zaben Fidda Gwani na 2023. Hoto: @DeleMomodu.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce mafi yawancin shugabannin jam'iyyar PDP daga kudu sun rika yi wa juna bita da kulli a maimakon hada kai wuri guda su tsayar da mutum guda da za su marawa baya don yankinsu da samu kujerar.

Kalamansa:

"Ban yi mamaki ba, na gaskiya na ke fada. Na yi imani da cewa kudu ko shugbannin kudu ba su yi aiki tare ba."

Ya ce:

"Kuma na yi gargadi, a ranar 20 ga watan Maris na rubuta wasikga ga Gwamna Wike - daya cikin gwamnonin mu masu nagarta, muna kiransa 'Mr Prudence, na shafe shekara guda daya da rabi a PortHarcourt ina aiki don tallata shi.
"Amma, ina sanar da cewa zan yi takarar shugaban kasa, sai alakar mu ta samu matsala. A lokacin ne na fara zargin yana da niyyar fitowa takarar shugaban kasa amma bai fada wa kowa ba amma na sani kuma na tura masa wasika."

Kara karanta wannan

Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

Momodu ya yi ikirarin cewa Gwamna Wike bai kula shi ba duk da ya tura masa wasika ya kuma tura wa manyan lauyoyin Najeriya - Mike Ozekhome da tsohon ministan Shari'a, Mohammed Adoke.

Ya kara da cewa:

"Na san mutane don haka ina samun bayanai. Na kira Wike na kuma tura masa wasika amma bai kula ni ba. Na fada masa hakan za ta faru, za su mara taron dangi."

Ya kuma kara da cewa yan siyasan da suka taimaka wa tsohon mataimaki shugaban kasa Atiku Abubakar ya zama dan takarar PDP ba su yi masa taron dangi ba.

Momodu ya ce:

"Ba su min taron dangi ba domin harka ce ta kudi, wasu lokutan za ka kashe kudi don aikin alheri, za ka kashe kudi duk da cewa ba dole kai ne za ka amfana ba. Duk abin da na samu, na kan kashe wa wasu mutane mafi yawansa."

Kara karanta wannan

Bayan ya gaza samun takara, Gwamna Wike ya fallasa abin da ya faru a zaben PDP da 2019

Dan jaridan ya yi bayanin

Kalamansa:

"Abin da na ke kokarin cewa shine yan Najeriya su koyi tallafawa mutanen kirki. Hasali ma, gwamna daya kacal daga kudu ya yi maraba da ni, sauran idan ka aika sako ba za su amsa ba, idan ka kira ba za su daga ba.
"Kuma na san ranan sakayya zai zo kuma ta zo ranar Asabar da ta gabata."
"Ni mutum ne wanda baya bata lokaci, kuma na iya dabara. Ban samu kuri'a ko daya ba ranar Asabar don ban biya kowa ko sisi ba."

2023: Gudaji Kazaure Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin APC a Jigawa, Akwai Yiwuwar Zai Koma NNPP

A wani rahoto, Muhammad Kazaure, fitaccen dan majalisar nan mai wakiltar mazabar Kazaure/Roni/Gwiwa da Yankwashi a Jihar Jigawa na majalisar tarayya bai samu tikitin tsayawa takara ba a jam’iyyar APC, Premium Times ta ruwaito.

Kazaure ya na da jikakkiya da Gwamna Muhammad Badaru na jihar, tare da kuma jam’iyyar, reshen jihar Mukhtar Zanna, shugaban karamar hukumar Kazaure ne ya kayar da shi.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Zanna ya samu kuri’u 89, na kusa da shi kuma Muhammad Zakari mai kuri’u 70 yayin da Kazaure ya samu kuri’u 26.

Muhammad Alhassan, wanda soja ne mai murabus, sannan ya rike mukamin Kwamishinan Noma a jihar, ya samu kuri’u 8, sai Abdullahi Mainasara mai kuri’u 7.

Asali: Legit.ng

Online view pixel