Bayan ya gaza samun takara, Gwamna Wike ya fallasa abin da ya faru a zaben PDP da 2019

Bayan ya gaza samun takara, Gwamna Wike ya fallasa abin da ya faru a zaben PDP da 2019

  • Gwamna Nyesom Wike ya ce da gwamnonin kudancin Najeriya aka hada-kai, aka doke shi a PDP
  • Nyesom Wike ya zargi mutanensa da taimakawa wajen ba Atiku Abubakar nasara a zaben gwani
  • ‘Dan siyasar ya ce a zaben 2019, shi kadai ne ya ki yarda ya hada-kai da APC domin ta samu 25%

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - A ranar Litinin aka ji Nyesom Wike yana zargin abokan aikinsa daga yankin kudancin Najeriya da taimakawa wajen rashin nasarar da ya samu a PDP.

Jaridar This Day ta rahoto Nyesom Wike yana mai cewa amfanin takararsa shi ne ya nunawa yankin Arewa cewa 'yan kudu su na da karfin da za su iya takara.

Da yake jawabi a garin Fatakwal a taron da aka shirya domin tarbarsa bayan zaben fitar da gwani, Wike ya ce na-kusa da Atiku ba su da wani nauyi a mizanin siyasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

Gwamnan ya nuna takaicinsa a kan yadda wasu abokan aikinsa daga kudancin Najeriya suka yi watsi da makomar yankinsu, su ka biyewa son zuciyarsu a zaben.

Meyasa Wike ya yi takara?

An rahoto Wike yana cewa ya shiga neman takara ne musamman saboda yarjejeniyar da aka cin ma tsakanin gwamnonin kudu cewa su ya kamata su karbi mulki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon Ministan ya zargi wadannan gwamnoni na yankinsa da yin abin kunya da yaudarar jama'ansu.

Nyesom Wike
Nyesom Wike a zaben PDP Hoto: PDPMEDIAVANGUARD
Asali: Facebook

“A duba yadda wani yanki su ka hada kansu, amma yankin na mu sun gagara hada-kai. Sai aka yi amfani da ku wajen murkushe mutanenku.”
“A haka ku na tunanin cewa kun yi nasara? Kun sha kasa! Za ku cigaba da zama bayi. Ka da ku damu mutanen Ribas, PDP ta na bukatarmu.”

- Nyesom Wike

Jaridar ta rahoto Wike yana cewa da an raina ‘yan kudu a siyasa, amma a sanadiyyar takararsa, ya girgiza jam’iyyar PDP, ya kuma hana kowa sakat a yankin.

Kara karanta wannan

Matasan Daura su na goyon bayan Kwankwaso ya karbi mulkin Najeriya bayan Buhari

Har ila yau, Gwamna Wike ya zargi wasu da cewa surukansu da ‘yanuwansu su na APC, amma kuma su na kokarin tsoma baki a kan harkokin jam’iyyar PDP.

Abin da ya faru a 2019

“A 2019 ni kadai ne gwamnan Kudu maso kudu da ban shiga yarjejeniya da gwamnatin nan ba. Da suka zo, na fada masu ba zan yarda da wannan ba.”
“Shiyasa a duk jihohin kudu maso kudu, shugaban kasa ya samu 35% zuwa 40% na kuri’un mutane. Ni kuwa na ce sam ba za ayi wannan da ni ba.”

Ya aka yi Atiku ya doke Nyesom Wike?

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya nemi zama ‘dan takarar shugaban kasa a PDP, amma Atiku Abubakar ya doke shi, gwamnan ne ya zo na biyu da kuri'u 230.

Ratar kuri’a 134 aka samu tsakanin Wazirin Adamawa da Gwamnan jihar Ribas wanda ya zo na biyu. Mun tattaro maku dalilan da suka taimakawa Atiku a zaben.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku ya yi amfani da dabara daf da mintin karshe, ya doke Wike a zaben fitar da gwani

Asali: Legit.ng

Online view pixel