Gudaji Kazaure ya rubuta korafi, ya yi bayanin silar rasa takarar komawa Majalisarsa

Gudaji Kazaure ya rubuta korafi, ya yi bayanin silar rasa takarar komawa Majalisarsa

  • Muhammad Gudaji Kazaure ya sha kashi a zaben tsaida ‘dan takarar Majalisar Wakilan Tarayya
  • Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ya ce Gwamna Badaru Abubakar ne ya kitsa rashin nasararsa
  • 'Dan Majalisar yana zargin APC ta sabawa dokoki wajen gudanar da zaben tsaida 'yan takaran Jigawa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jigawa - Muhammad Gudaji Kazaure mai wakiltar Kazaure/Roni/Yankwashi/Gwiwa a majalisar tarayya ya zargi gwamnan Jigawa da jefa APC a hadari.

Premium Times ta rahoto Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure yana mai zargin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar da shiryawa APC zagon-kasa.

Hakan na zuwa bayan Muhammad Gudaji Kazaure ya sha kashi a zaben tsaida gwani na ‘dan majalisar wakilan tarayya, ya zo na uku a zaben da aka yi.

A wani korafi da Kazaure ya rubutawa hukumar INEC a farkon makon nan, ya yi zargin cewa an ki yi masa adalci tun wajen zaben masu fitar da ‘dan takara.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

Aikin Gwamna ne - Kazaure

‘Dan majalisar ya godewa Allah game da damar da ya ba shi, ya bayyana cewa Gwamna ya saba doka wajen zaben masu tsaida ‘dan takara a yankin Kazaure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun wancan lokaci ya ce Mai girma gwamnan ya ba ‘ya ‘yan jam’iyyar umarni ka da su zabe shi a matsayin ‘dan takara a zaben da ya kira wasan kwaikwayo.

Gudaji Kazaure ya ce ya kira zaben da wasan kwaikwayo ne domin ba a bi abin da sabuwar dokar zabe ta ce ba, kuma hakan zai yi wa jam'iyya illa a nan gaba.

Gudaji Kazaure
Hon. Gudaji Kazaure Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Kira ga magoya bayansa

A karshe, ‘dan siyasar ya yi kira ga magoyansa a gida da kasar waje da cewa ka da su tada hankalinsu domin har gobe talakawansa na tare da shi.

Baya ga kira ga magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, Kazaure ya ce za a ga abin da zai biyo baya, wanda a na shi hangen, zai jefa APC ne a cikin matsala.

Kara karanta wannan

APC: Dan majalisan Arewa da ake zargi da badakalar kudin Korona ya rasa tikitin tazarce

Shahararren ‘dan majalisar ya zargi Gwamna mai-ci da neman ganin bayansa duk da biyayyar da yake yi masa, don haka ya ce zai nemi hakkinsa a turbar doka.

Idan ana so a doke ‘dan majalisar mai wakiltar Kazaure/Roni/Yankwashi/Gwiwa da kasa, ya ce dole sai APC ta zabi masu tsaida mata ‘yan takara na hakika.

Za a canza Sanatocin Katsina?

A baya kun ji labari cewa jam’iyyar APC mai mulki ta canza wadanda za su yi mata takarar Sanata a duka bangarorin da ke jihar Katsina a zabe mai zuwa

Hon. Nasir Zangon Daura zai nemi Sanata a shiyyar Daura, Muntari Dan Dutse ya tika Sanata mai-ci, Bello Mandiya da kasa, haka zalika an doke Kabiru Barkiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel