Yadda duka Sanatocin Katsina 3 su ka rasa tikitin tazarce a karkashin Jam’iyyar APC

Yadda duka Sanatocin Katsina 3 su ka rasa tikitin tazarce a karkashin Jam’iyyar APC

  • Kanal Abdulaziz Musa ‘Yaradua (rtd) ya samu tikitin takarar Sanata a bangaren Katsina ta tsakiya
  • A shiyyar Kudancin jihar Katsina kuwa, Hon. Muntari Dan Dutse ne zai yi wa APC takara a 2023
  • Nasir Zangon Daura ya samu tikitin APC a yankin Daura bayan sauya-shekar Ahmad Babba-Kaita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Kanal Abdulaziz Musa ‘Yaradua (mai ritaya) ya yi nasara a wajen lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina.

Abdulaziz Musa ‘Yaradua ya doke Sanata Abdullahi Barkiya wajen samun tikitin majalisar dattawa, shi ne wanda zai yi wa APC takara a zaben 2023.

Jaridar 21st Century Chronicle ta fitar da wannan rahoto a ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu 2022.

Kanal ‘Yaradua wanda aka fi sani da Audu Soja ya dade yana neman takara a Katsina, wannan karo za a gwabza da shi a zaben ‘dan majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 10 da suka jawo Atiku Abubakar ya dankara Wike da kasa a zaben PDP

A zaben 2015, Audu Soja ya nemi takarar Sanatan jihar Katsina ta tsakiya a jam’iyyar APC, amma sai ya sha kashi a hannun Sanata Umar Ibrahim Kurfi.

Haka zalika da ya sake yin takara a 2019, tsohon sojan ya sha kashi wajen Sanata Abdullahi Barkiya, amma wannan karon Sanata mai-ci ya rasa tuta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kanal Audu Soja Hoto: Sojanetwork
Abdulaziz Musa 'Yardua Hoto: Sojanetwork
Asali: Facebook

Rahoton ya ce ‘Yaradua ya tashi da kuri’u 310, Umar Ibrahim Kurfi ya samu kuri’a 197, shi kuma wanda ke kan kujerar, Abdullahi Barkiya ya samu kuri’a 70.

Tsohon mai ba gwamnan jihar Katsina shawara, Binta Abba Dutsinma ta tsira da kuri’a daya tal.

Kafin a shiga zaben, tsohon ‘dan majalisar tarayya, kuma Mai ba Gwamna shawara a kan harkokin siyasa, Hon. Kabiru Shuaibu Charanci ya janye takara.

APC ta canza ‘yan takaran Sanatoci

A shiyyar kudancin Katsina, Hon. Muntari Dan Dutse ya yi galaba a kan Sanata Bello Mandiya. Hon. Dan Dutse ya doke Sanata mai ci da ratar kuri’u fiye da 280.

Kara karanta wannan

‘Yaradua, Ganduje, El-Rufai, Bafarawa: 'Ya 'yan Fitattun 'Yan Siyasa Masu Takara a 2023

‘Dan majalisar Zango/Baure, Nasir Sani Zangon Daura shi ne zai yi wa APC takarar Sanata a yankin Daura bayan ya doke tsohon kwamishina, Mustapha Kanti.

Babba Kaita zai yi takara a PDP

Ku na da labari Sanata Ahmed Babba Kaita zai sake neman takarar majalisar dattawa na shiyyar Arewacin Katsina, wannan karo ‘Dan majalisar zai tsaya ne a PDP.

Jam’iyyar PDP ta tsaida Babba Kaita ya yi mata takarar Sanata a 2023, bayan ya fice daga APC. Shi kadai ne Sanata mai-ci da zai nemi tazarce a shekara mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel