Tinubu: Babu wani cin girma da zan yi, burina kawai na yi takara a zaben 2023 mai zuwa

Tinubu: Babu wani cin girma da zan yi, burina kawai na yi takara a zaben 2023 mai zuwa

  • Rahotanni sun bayyana cewa Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya sha alwashin ba zai janye wa kowane dan takara ba
  • An ruwaito dan takarar shugaban kasan na jam’iyyar APC ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin tantance 'yan takara
  • An ce ya shaida wa mambobin kwamitin tantance 'yan takaran cewa ba zai amince da wata matsaya da za a zo da ita ba ta cewa ya daga kafa

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa Bola Tinubu ya dage kan cewa ba zai janye daga takara ba duk kuwa abin da zai faru.

An ce dan takarar na kan gaba a jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika

Jaridar Leadership ta yi ikirarin cewa Tinubu ya bayyanawa kwamitin cewa ba zai amince da wata matsaya da za a zo da ita kan 'yan takara ba.

Wannan ikirari da jaridar ta yi ba lallai ya zama tabbas ba saboda kwamitin bai bari 'yan jarida su shiga wurin da aka yi taron tantancewar ba.

Yadda aka kaya da Tinubu a taron tantance 'yan takara
Tinubu: Babu wani cin girma da zan yi, burina kawai na yi takara a zaben 2023 mai zuwa | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban na jam’iyyar APC na kasa na daga cikin mutane 12 da aka tantance daga 'yan takarar shugaban kasa a jiya, kamar yadda rahoton kafafen yada labarai da dama ya bayyana.

An tantance 'yan takara 12

Ya zuwa yanzu dai ’yan takarar shugaban kasa 12 ne aka tantance, wadanda suka hada da Tinubu; ministan sufuri, Rotimi Amaechi; Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru; tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani da tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba.

Hakazalika da tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun; fitaccen faston nan na Legas kuma tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasan Muhammadu Buhari a zaben 2011, Fasto Tunde Bakare.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Sauran sun hada da gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi; tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yerima; Sanata Ajayi Boroffice; mace daya tilo, Barr (Mrs) Uju Kennedy Ohnenye, da Fasto Nicholas Felix Nwagbo, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Jigo ne a APC, amma jam'iyya bai kamata ta zabi laku-laku ba

Da wakilin Legit.ng Hausa ya tattauna da mai sharhi kan siyasa, kuma mamban APC a jihar Gombe Sani Muhammad Yakubu, ya ce zaben fidda gwanin PDP ya zama gwaji ga jam'iyyar APC da mambobinta, duba da wanda PDP ta ba tikiti.

A cewarsa:

"Ba wai cika baki ko bugun kirji bane namu, ya rage wa manyanmu su zabi kwararre a siyasa da zai ya ja da Atiku, duk da ma dai shi Tinubu ya yi fice.
"Amma fa, mun gwammace a zabi wanda ba laku-laku ba.
"Laku-laku shi ne wanda ba lallai ya iya kawo kujerar shugaban kasa ba, ma'ana wanda gajiyayye ne.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An bukaci kwamiti ya kori Tinubu daga takaran shugaban kasa a APC

"Burinsa ya gaji Buhari, burinmu a samu shugaba a karkashin APC mai nagarta, shikenan."

Babbar magana: An bukaci kwamiti ya kori Tinubu daga takaran shugaban kasa a APC

A wani labarin, an bukaci kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ya kori Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas, saboda alamomin tambaya game cancantar iliminsa, TheCable ta ruwaito.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan Mayu 17, 2022, wani Sagir Mai Iyali, wanda ya bayyana kansa a matsayin dan APC daga jihar Kano, ya roki jam’iyyar da ta haramtawa Tinubu takara kan wasu takardun karya da ya mika wa INEC a 1998.

John Oyegun, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ne ke jagorantar kwamitin tantancewar, kuma ana ci gaba da atisayen ne a Transcorp Hilton da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel