Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

  • Rigima ya barke tsakanin Tsohon Gwamna Adamu Aliero da mai zamani Atiku Abubakar Bagudu
  • Sanata Aliero wanda ke majalisa yanzu ya ce Gwamnan ya dade yana raina masa hankali
  • Aliero ya zargi Gwamna Bagudu don rubuta sunayen deleget da kansa don su zabi wanda yake so

Kebbi - Yayinda ake shirin gudanar da zaben fidda gwanin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kebbi, Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero, yace ya janye daga takarar.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Aliero ya fitar kuma ya baiwa kamfanin dillancin labarai NAN a Birnin Kebbi ranar Asabar.

Yace shi fa mutum ne mai son zaman lafiya da hadin kan jama'a saboda haka ya janye ne bisa wasu dalilai masu yawa.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku ya yi amfani da dabara daf da mintin karshe, ya doke Wike a zaben fitar da gwani

Fito na fito da Gwamna Bagudu
Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata Hoto: Aliero Bagdu
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jawabin, Aliero ya yi zargin cewa Gwaman jihar, Atiku Bagudu, ne ya zabi Deleget din da zasu kada kuri'a gaba daya.

A cewarsa:

"Ina mai sanar da cewa na janye daga takarar zaben fidda gwanin Sanata ta tsakiya karkashin APC."
"Zaben da aka shirya na bogi ne saboda jerin deleget din da aka fitar Gwamnan jihar ya zabesu daya bayan daya don suyi abinda yake so."
"Na dade ina hakuri da tsokanar da gwamnan ke min kuma abin ya wuce gona da iri."

Aliero ya karkare jawabinsa da cewa shi da mabiyan zasu san tayi yanzu.

Alaka ta yi tsami tsakanin Aliero da Gwamna Bagudu kan wanda zai mallaki tikitin APC

A bayan kun ji cewa alaka ta yi tsami a tsakanin Aleiro da Bagudu tun bayan tarukan jam’iyyar mai mulki a jihar. Shugabannin biyu na fafatawa kan wanda zai ja ragamar tsarin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

Dan majalisar ya koka kan tursasa yan takara a yayin taronsu da tsige mambobin jam’iyyar da ake ganin suna biyayya gare shi a tsarin shugabannin jam’iyyar.

Da yake magana a yayin gangamin siyasa a watan Janairu, Aliero ya ce rikicin siyasa na jiran APC a jihar idan jam’iyyar ta ki yin adalci a tsakanin mambobinta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel