2023: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a NNPP Ya Sallama Wa Kwankwaso, Amma Ya Nemi Wata Alfarma Daga Kwankwason

2023: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a NNPP Ya Sallama Wa Kwankwaso, Amma Ya Nemi Wata Alfarma Daga Kwankwason

  • Mai neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ya ce ya sallama wa Kwankwaso takarar
  • Amma ya kuma nemi alfarma cewa Kwankwason ya dauke shi a matsayin mataimakinsa su yi takarar zaben tare a 2023
  • Olufemi Ajadi ya bayyana Kwankwaso a matsayin dan Najeriya mai kishin kasa kuma jajirtacce wanda zai fitar da Najeriya daga kangin da ta shiga idan an zabe shi

Abeokuta - Mr Olufemi Ajadi, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwa jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya sanar da janyewarsa daga takarar, Daily Trust ta rahoto.

Premium Times ta rahoto cewa Mr Ajadi ya shaida wa yan jarida a Abeokuta, Jihar Ogun, a ranar Alhamis cewa ya janye daga takarar ne don mara wa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso baya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

2023: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a NNPP Ya Janye Wa Kwankwaso, Amma Ya Gabatar Da Wata Buƙata
2023: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a NNPP Ya Janye Wa Kwankwaso. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yana fatan zama mataimakin Kwankwaso a babban zaben na 2023.

"Ni Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, bayan la'akari da abubuwa da dama, don kuma cigaban jam'iyyar mu da kasarmu, na janye takara ta ta shugaban kasa domin goyon bayan takarar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin abokin takararsa," in ji shi.
"Sanata Kwankwaso jajirtaccen dan Najeriya ne, dan siyasa kuma shugaba wanda zai kawo cigaba a kasar nan."

Da ya ke magana kan halin da Najeriya ke ciki, Mr Ajadi ya ce babu wani abu da ke aiki a kasar.

"Najeriya kasa ce da Allah ya sawa albarka, amma duba halin da muke ciki yanzu, za ka yarda cewa abubuwa ba su aiki yadda ya dace.
"Akwai rashin tsaro, duk da cewa akwai gwamnati a kasar tare da yan sanda, sojojin kasa, sojojin ruwa da sojojin sama.

Kara karanta wannan

Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023

"Yaran mu sun gama makaranta babu aiki. Kana mamakin ganin laifuka suka yi yawa? Babu tituna masu kyau. Babu ruwa, babu lantarki da sauran abubuwan more rayuwa. Amma muna da gwamnati. Muna da biliyoyin naira da kadarori. Ina tambaya, Ina matsalar ta ke?.
"Ya ku yan Najeriya, matsalar itace son kai."

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

A wani rahoton, mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel