Sokoto: Dan takarar gwamna ya yi baram-baram da Tambuwal, ya fice daga PDP
- Siyasar PDP dai na ci gaba da daukar wani salo mai jan hankali, ana ci gaba da samun dirkaniya a wasu jihohin
- Dan takarar gwamna a jihar Sokoto ya yi saraf ya fice daga PDP saboda wasu dalilai na siyasa da ba su mishi dadi ba
- Hakazalika, rahoton da muke samu ya bayyana cewa, dan takarar ya yi baram-baram da gwamna mai ci a jihar Sokoto
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sokoto - Wani babban jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Sokoto, Mukhtari Shehu Shagari, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
Dan siyasar na daya daga cikin manyan yan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar ta PDP.
Shagari, wanda ya kasance tsohon ministan albarkatun ruwa na jihar Sokoto kuma tsohon mataimakin gwamna ya sanar da ficewarsa jim kadan bayan taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar da aka yi.
Taron wanda Gwamnan jihar ya jagoranta ya tsayar da tsohon sakataren gwamnatin jihar a matsayin dan takarar gwamna na PDP a zabe mai zuwa, jaridar Punch ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shagari a wani jawabi dauke da sa hannunsa, ya zargi gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da aikata ha’inci.
Ya ce:
“Ina burin sanar da ku cewa Ni, Mukhtari Shehu Shagari daga yau na tashi daga dan jam’iyyar Peoples Democratic Party.
“Wannan hukuncin mai tsauri ya kasance ne sakamakon jerin cin amana da na fuskanta a hannun jam’iyya da ke ikirarin karya cewa tana kan tafarkin damokradiyya amma maimakon haka ta zama jam’iyyar kulla ciniki da wanda ya fi sakin kudi ba tare da la’akari da aiki, jajircewa, sadaukarwa, zuba jari da hidimar da mutum ya yiwa jam’iyyar tun 1998 ba.
“Baya ga tarin sadaukarwar da nayi da hidimtawa jam’iyyar, PDP da ake magana a kanta bata da tsarin sakawa mutum da alkhairi.”
Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano
A wnai labarin, Mohammed Abacha, dan marigayi tsohon shugaban kasa, Sani Abacha, ya lashe zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kano.
Jami'ar zabe, Barista Amina Garba, ta ayyana Mista Abacha a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ya samu kuri’u 736 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa, Sani-Bello wanda ya samu kuri’u 710, PM News ta rahoto.
Shugaban kwamitin zaben, Mohammed Jamu, ya ce an gudanar da zaben fidda gwaninsu bisa ka’ida tare da zababbun deleget sannan hukumar zabe ta kasa (INEC), yan sanda da Jami’an DSS suka sanya idanu.
Asali: Legit.ng