Da duminsa: Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano

Da duminsa: Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano

  • Dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Mohammed Abacha, ya yi nasara a zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano
  • Abacha ya samu kuri'u 736 wajen yin nasara kamar yadda jami'ar zabe, Barista Amina Garba, ta bayyana
  • Shugaban kwamitin zaben, Mohammed Jamu, ya ce an gudanar da zabukan nasu ne bisa ka’ida tare da sahihan deleget

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Mohammed Abacha, dan marigayi tsohon shugaban kasa, Sani Abacha, ya lashe zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kano.

Jami'ar zabe, Barista Amina Garba, ta ayyana Mista Abacha a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ya samu kuri’u 736 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa, Sani-Bello wanda ya samu kuri’u 710, PM News ta rahoto.

Da duminsa: Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano
Da duminsa: Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano Hoto: thegeniusmedia.com.ng
Asali: Facebook

Shugaban kwamitin zaben, Mohammed Jamu, ya ce an gudanar da zaben fidda gwaninsu bisa ka’ida tare da zababbun deleget sannan hukumar zabe ta kasa (INEC), yan sanda da Jami’an DSS suka sanya idanu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Akanta janar din jihar Ribas ya lashe tikitin gwamnan PDP

Daily Nigerian ta rahoto cewa jami’an INEC shida da suka hada da mataimakiyar darakta da ke kula da zabe da sanya idanu kan jam’iyyu a hedkwatar INEC, Hauwa Hassan; sakataren gudanarwa na jiha, Garba Lawal; shugaban sashin shari'a, Suleiman Alkali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sune Shugaban ayyukan zabe, Sule Yaro; shugaban sashin rijistan masu zabe, Ocheke Edwin da shugabar sashin kudi, Hassan Dalhatu.

Yayin da aka gudanar da zaben fidda gwanin da ya samar da Abacha a matsayin dan takara a hedkwatar jam’iyyar da ke Lugard Avenue Kano, wani zaben fidda gwanin na gudana a cibiyar matasa ta Sani Abacha, a babbar birnin jihar.

An tattaro cewa har yanzu ana kada kuri’u a zaben fidda dan takarar na cibiyar matasa ta Sani Abacha.

Wadanda ke takara a wannan zaben fidda gwanin sun hada da Yunusa Dangwani, Yusuf Dambatta, Muaz Magaji, Ibrahim Ali-Amin, Sadiq Wali da Mustapha Getso.

Kara karanta wannan

'Dan Sule Lamido ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan Jigawa

Shehu Sani ya sha kashi a zaben ‘dan takarar Gwamnan Kaduna, ya tsira da kuri’u 2

A wani labarin, mun ji cewa burin Shehu Sani na zama sabon gwamnan jihar Kaduna a 2023 ba zai cika ba, a sakamakon rashin nasarar da ya yi a zaben fitar da gwani.

Rahoton da muka samu ya tabbatar da cewa Sanata Shehu Sani bai iya samun tikitin PDP ba. ‘Dan siyasar ya tabbatar da wannan a Twitter da asuban ranar Alhamis.

Sani ya taya wanda ya yi nasara murna, ya yabawa wadanda suka ba shi kuri'arsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel