Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

  • Rikici ya barke a jam'iyyar PDP ta jihar Neja a lokacin da ake ci gaba da shirin zaben fidda gwanin gwamna
  • Wannan lamari ya haifar cece-kuce da zanga-zanga daga wasu 'yan takarar gwamnan jam'iyyar ta PDP
  • Ya zuwa yanzu dai, an dage zaben zuwa wani lokaci domin daidaitawa da kashe wutar da ta taso

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Neja - Jam'iyyar adawa ta PDP ta dage zaben fitdda gwani da ke gudana a jihar Neja, biyo bayan wata zanga-zanga da ta barke, inji rahoton Daily Trust.

Zaben da aka shirya gudanarwa a yau Laraba ya koma Alhamis bayan zanga-zangar da hudu daga cikin biyar da ke takara suka tayar.

Rahoto ya bayyana cewa an fara samun matsala ne yayin da hudu daga cikin biyar din suka nuna rashin gamsuwa da jerin sunayen deliget-deliget da za su kada kuri'a, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan janyewa daga takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga PDP

PDP a Neja ta kama da wuta
Jihar Neja: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Majiya ta tattaro cewa zanga-zangar ta biyo bayan kalaman da ke cewa da daya daga cikin ‘yan takarar Alhaji Isah Liman Kutigi shi ne zabin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meye matakin da ake dauka?

A lokacin da lamari ya yi kamari, wasu masu son tsayawa takara sun fice daga wurin taron.

Shugaban Kwamitin Zabe, Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo, ya gayyaci shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 25 da su yi wata ganawar sirri domin kashe wutar da ta kama.

Bayan taron, Mista Ewhrudjakpo, ya sanar da dage zaben zuwa ranar Alhamis.

Hudu daga cikin masu neman takara biyar din; Idris Sani Kutigi, Alhaji Abdullahi Isah Jankara, Barista Abdulrahman Gimba, da Sidi Abdul, an ce sun dage kan cewa ba su amince da sahihancin jerin sunayen deliget ba.

Kana sun bukaci kwamitin zaben da ya nemi deliget-deliget din da su gabatar da sahihan hanyoyin tantancewa kafin su yi zaben.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Shahararren gwamnan Arewa ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan PDP

An tattaro cewa kowane deliget zai gabatar da katin zabe ko na shaidan zama dan kasa a wurin domin tantance sunayensu.

Gwabzawar 2023: Fintiri ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan PDP a Adamawa

A wani labarin, gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar.

Channels Tv ta ruwaito cewa, gwamnan jihar ya yi nasara da jimillar kuri’u 663 daga cikin 668 da kuri’u 5 daga cikin kuri’un da aka kada.

Gwamnan, wanda ya sanar da sake tsayawa takara a watan Afrilu, ya ce zai ci gaba da kokarin raya jiha kamar yadda gwamnatinsa ta tsara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel