2023: Da gaske fa nake ina son gaje Buhari, cewar Tinubu ga sarakunan gargajiya

2023: Da gaske fa nake ina son gaje Buhari, cewar Tinubu ga sarakunan gargajiya

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Tinubu ya bayyana bukatarsa ta son gaje Buhari, inda yace ba da wasa yake takara ba
  • Ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wata ziyara jihar Edo domin neman goyon baya da albarkar sarakunan gargajiya
  • A bangare guda, basaraken gargajiya ya shawarci ' yan siyasa da su guji fadin abubuwan da ba za su iya ba lokutan kamfen

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Benin, Jihar Edo - Jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba wasa yake ba a burinsa na zama shugaban kasa, ya kara da cewa al’ummar kasar nan na bukatar shugaban da zaai kawo sauyi irin sa a 2023.

Tinubu wanda ya je Benin, babban birnin jihar Edo a karshen mako domin neman bakin wakilan APC gabanin fidda gwani, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Oba na Benin a fadarsa.

Kara karanta wannan

Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi

Tinubu ya magantu kan takararsa
2023: Da gaske fa nake ina son gaje Buhari, cewar Tinubu ga sarakunan gargajiya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Depositphotos

A cewar Tinubu:

"Ni ne wanda ya fi cancanta da dacewa na tsayawa takarar shugaban kasa da kuma jagorantar al'ummar kasar nan wajen magance matsalolin tattalin arziki da tsaro."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam’iyyar APC ta tsayar da ranakun 29 da 30 ga watan Mayu domin gudanar da zabukan fidda gwani na shugaban kasa gabanin zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya ce:

“Ba wasa nake yi da burina na zama shugaban kasa ba, ina son zama shugaban kasa. Ina nan fadar ne don neman albarka da addu'arku na zama dan takarar jam'iyyar APC kuma a karshe na zama shugaban kasa. Na san ma'anar albarkar ku da yarjewarku."

Da yake mayar da martani ga batun Tinubu, Oba na Benin, Oba Ewuare II, ya shawarci ’yan siyasa da su mayar da hankali kan manufofin da za su iya cimmawa a madadin jero abubuwan da ba za su iya cimma ba, rahoton Tribune Online.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

2023: 'Yan kwamiti sun haramtawa tsohon Sanatan PDP shiga zaben neman Gwamna a APC

A wani labarin, Kwamitin da ke tantance ‘yan takarar jam’iyyar APC a jihar Kuros Riba, ya haramtawa Sanata Bassey Otu shiga zaben gwamna a 2023.

Kamar yadda labari ya je wa jaridar nan ta The Cable, Sanata Bassey Otu ba zai iya shiga zaben fitar da gwanin zama ‘dan takarar gwamna a Kuros Ribas ba.

Ana tunani an hana ‘dan siyasar yin takara a jam’iyyar ta APC mai mulki ne saboda ya gagara kawowa kwamitin takardar kammala firamare da na WASC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel