Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi

Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi

  • Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC kuma gwamnan Jihar Ekiti, Mr Kayode Fayemi ya sanar da wakilan jam’iyyar cewa ba ya da kudi amma ya na tausayin ‘yan Najeriya
  • Ya bayyana hakan ne a Jihar Kaduna ranar Alhamis inda ya yi alkawarin kawo karshen duk wani rashin tsaro da ta’addanci da zarar an zabe shi a matsayin shugaban kasan Najeriya
  • A cewarsa, ya yarda da cewa zai iya dasawa daga inda shugaban kasa ya tsaya saboda yana da iko, cancanta da kuma tsananin jin-kai ga jama’a wanda zai ba shi damar shugabanci na kwarai

Kaduna - Mr Kayode Fayemi, dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar APC kuma yanzu haka gwamnan Jihar Ekiti ya ce ba ya da kudi amma yana da cancanta, dagewa, jajircewa da tausayi ga ‘yan Najeriya da za su ba shi damar shugabantar kasar.

Kara karanta wannan

Manjo Hamza Al-Mustapha: Ina gaje Buhari zan tare a dajin Sambisa saboda dalilai

A cewarsa, shi ba mai kudi ba ne, amma yasan shugabancin Najeriya ba na masu kudi ba ne, Vanguard ta ruwaito.

Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi
Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Fayemi. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana hakan ne a Kaduna ga wakilan APC a ranar Alhamis inda ya yi alkawarin kawo karshen duk wani rashin tsaro idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Gwamna Fayemi ya ce zai kawo karshen matsalolin Najeriya kamar rashin daidaito, fatara da tabarbarewar tattalin arziki, wadanda su ne manyan matsalolin da ya dace a gama da su kafin rashin tsaro.

Ya ce ya na so ya ci gaba daga inda Buhari ya tsaya

A cewarsa:

“Jihar Kaduna tana daya daga cikin jihohin da ke samar da abinci a kasar nan. Muna son shigar da matasanmu cikin harkokin noma sannan mu kawo hanyar girmama manomanmu da kuma shigar da kayan nomansu.

Kara karanta wannan

Tambuwal: 'Kebura' Ƴan Najeriya Ke Sha a Mulkin Buhari

“A matsayina na daya daga cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar APC, na ga dacewar samar da hulda tsakanin wadanda su ka yi wa jam’iyyar aiki da wadanda su ka amfana da jam’iyyar.
“Na zo nan ne don na tabbatar muku da cewa ina son dasawa daga inda shugaban kasa ya tsaya kuma na yarda da cewa zan iya, ina da jajircewa da kuma jin-kai ga mutanenmu wanda zai ba ni damar shugabancin kasar nan dakyau. Ba kara-zube na shiga siyasa ba, sai da na yi ilimi mai zurfi.”

Fayemi ya bayyana kalubalen da ya fuskanta da dadewa

Ya bayyana yadda ya yi aiki da Radio Kudirat inda ya fuskanci kalubale iri-iri duk don ganin Najeriya ta ci gaba, kamar yadda Vanguard ta nuna.

Ya shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu dubi akan duk ‘yan takarar shugaban kasa, su duba cancanta da kuma dagewarsu sai su zabi wanda ya fi dacewa.

Kara karanta wannan

Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya

Ya ce ba ya kudi amma ya san cewa aikin da Najeriya ta ke bukata ba na mai kudi ba ne. Sai dai zai iya tara kudi kasancewar akwai abokansa da su ka yarda da shi wadanda za su taimaka masa wurin ganin an kai gaci.

A cewarsa, bai tsaya takara don ya tatsi asusun kasar nan ba face sai don kawo ci gaba, bunkasa tattalin arziki da kuma samar da ababen more rayuwa da tsaro a kasar nan.

“Mun zanta da El-Rufai duk da ya ce ya gaji kuma yana bukatar hutu, amma ba a gama aikin ba. Ana bukatar sa hannunsa don kawo ci gaban kasar nan,” in ji Fayemi.

A bangaren El-Rufai, ya ce Fayemi mutumin kirki ne mai matukar hakuri. Kuma ya san shi fiye da shekaru 20 da su ka shude.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

Kara karanta wannan

Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel