An Kai Wa Ɗan Takarar Gwamna Da Tawagarsa Hari, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

An Kai Wa Ɗan Takarar Gwamna Da Tawagarsa Hari, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

  • Wasu bata gari da ake kyautata zaton yan daban siyasa ne sun kai wa jerin gwanon motoccin dan takarar gwamnan APC na SDP a Jihar Ekiti hari
  • Jackson Adebayo, mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Segun Oni ne ya tabbatar da harin yana mai cewa bata garin sun kai harin ne da bindigu da adduna da sanduna
  • A bangarensa, Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu ya tabbatar da afkuwar harin da aka kai wa magoya bayan Oni

Ekiti - Wasu da ake zargin yan daban siyasa ne sun kai wa tawagar dan takarar gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Segun Oni, hari a karamar hukumar Efon Alaaye ta Jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Bayan ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22

An Kai Wa Ɗan Takarar Gwamna Da Tawagarsa Hari, Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Ekiti: An Kai Wa Ɗan Takarar Gwamna Na SDP Da Tawagarsa Hari, Ya Tsallake Rijiya Da Baya. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa direktan watsa labarai na kamfen din Segun Oni, (SOCO), Jackson Adebayo, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adebayo ya ce harin ya faru ne misalin karfe 3.30 na yammacin ranar Laraba.

Magoya bayansa da yan jam'iyya sun tarbarsa ne a lokacin da maharan suka afka musu, Jackson

Ya ce jim kadan bayan mambobin jam'iyyar na SDP da magoya bayansa sun taru domin tarbarsa, yan daban suka afka musu da adduna da sanduna sannan suna harbe-harbe da bindiga.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu ya tabbatar da afkuwar harin amma bai yi karin bayani ba.

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel