Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

  • Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar bai je taron sirrin da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya yi da wasu masu neman takarar shugaban kasa a PDP ba
  • An tattaro bayanai akan yadda suka tsawaita taron don neman yadda zasu bullo wa lamarin tsayar da dan takara don gudun tashin tarzomar cikin jam’iyyar
  • Cikin wadanda suka halarci taron da aka yi a gidan gwamnatin Port Harcourt akwai Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, Aminu Waziri Tambuwal da sauransu

Port Harcourt - Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Wike ya jagoranci gwamnonin PDP zuwa wajen Janar Babangida da Abdussalami

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP
Wike da wasu masu neman takarar shugaban kasa a PDP. Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Wike ya ce suna kokarin kawo hadin kai ne

Wike ya ce duk ‘yan takarar suna da burin kawo hadin kai yayin da zaben fidda gwani ya ke kara karatowa da kuma zaben kasa baki daya.

Gwamnan ya nuna burinsa na kawo ci gaba don jam’iyyar ta samu ta lashe babban zaben da za ayi na shugaban kasa a 2023 bisa ruwayar The Nation.

A cewarsa:

“Muna da burin kawo hadin kai a jam’iyyar. Burin mu shi ne mu faranta wa ‘yan Najeriya rai a shekarar 2023 yayin da PDP za ta amshi mulki don duk ‘yan Najeriya sun kosa.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau

“Ina mai tabbatar muku da cewa za mu hada kai wurin faranta wa duk ‘yan Najeriya rai.”

'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom din Takarar Shugabancin Ƙasa

A bangare guda, wata kungiya mai suna Abokan Tambuwal sun siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.

PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel