Duk da Shugaban kasa ya sa baki, har yanzu APC na fama da rikicin cikin gida a jihohi

Duk da Shugaban kasa ya sa baki, har yanzu APC na fama da rikicin cikin gida a jihohi

  • Wasu daga cikin ‘ya ‘yan APC a jihohin kasar nan su na iya sauya-sheka zuwa jam’iyyun hamayya
  • Rigingimun da ake ta fama da su a Kano, Zamfara, Kwara da wasu jihohi bai zo karshe ba har yau
  • ‘Ya ‘yan jam’iyya sun ki janye karar da suka shigar a kan APC duk da shugaban kasa ya yi magana

Abuja - Rikicin da ya dabaibaye APC a akalla jihohi 12 bai zo karshe. Jaridar Punch ta fahimci wannan, kuma ta fitar da rahoto na musamman.

Duk da irin kokarin da shugaban kasa, Mai Mala Buni da Abdullahi Adamu suka yi na ganin an sharewa kowa hawaye a APC, akwai sauran aiki.

Kwamitin sulhu da Sanata Abdullahi Adamu ya jagoranta bai gabatar da rahoton bincikensa ga CECPC ba, har yanzu akwai shari’o’i a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin da suka yi nasara, da wadanda suka sha kasa a zaben jam’iyyar APC

APC za ta rasa mutane a Kwara

A jihar Kwara, ‘yan tawaren da ke tare da Lai Mohammed sun cire tutar jam’iyyar APC daga sakatariyarsu. Hakan na nuna yiwuwar sauya-sheka.

Hon. Saheed Popoola daya daga cikin jiga-jigan da ke tare da bangaren Mohammed ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC kwanan nan, ya bi SDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren yada labarai na ‘yan tawaren APC a Kwara, Ibrahim Sharafadeen ya tabbatarwa Punch sun bar APC, amma ba su shiga wata jam’iyya ba tukun.

Shugaban kasa
Shugaban kasa da shugabannin APC Hoto: Bashir Ahmad / @bashahmad
Asali: Facebook

An yi shugabanni a Sokoto

Rahoton ya ce a jihar Sokoto ana ta fama da rigingimu har yanzu. Sai a makon nan ne ake ji cewa an rantsar da sababbin shugabannin APC a jihar.

Wani ‘dan jam’iyyar APC a Sokoto ya shaidawa manema labarai cewa PDP ta na zawarcinsu.

Kara karanta wannan

Abin da wasu wadanda suka yi takara a APC suke fada, bayan sun sha kashi a zaben kasa

Akwai kura a jihar Zamfara

A Zamfara kuwa, bangaren Bello Matawalle ne jam’iyyar APC ta sani. Mutanen Kabiru Marafa da Abul’Aziz Yari sun ki janye kara da su ka kai a kotu.

Mai magana da yawun wasu ‘yan tawaren APC a Zamfara ya ce sam ba su yarda cewa Tukur Danfulani ne shugaban jam’iyya ba, su na da ja da shi.

Yaran Aregbesola ba za su bar APC ba

Duk runtsi yaran Rauf Aregbesola ba za su fice daga APC a jihar Osun ba. Abiodun Agboola ya bayyana wannan, ya ce su na jiran hukuncin kotu ne.

Agboola ya ce ‘yan bangarensa sun shigar da kara a Abuja, su na kalubalantar takarar Gboyega Oyetola, su na sauraron hukuncin da za a zartar tukun.

'Yan G7 v tsagin Ganduje

Legit.ng Hausa ta fahimci haka lamarin yake a jihar Kano. Rahotanni sun nuna ba a yarda da kowane bangare a wajen zaben jam’iyya na kasa ba.

Kara karanta wannan

Shekara 1 da komawa APC, an dauki mukami mai tsoka, an damkawa tsohon ‘Dan adawa

A safiyar Talata ne ake ji Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin wanda ke tare da G7, ya ziyarci sabon shugaban JAPC na Kasa Sanata Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel