Gangamin taron APC: Buhari ya aika gagarumin sako ga Adamu, Omisore da sauran zababbun shugabanni

Gangamin taron APC: Buhari ya aika gagarumin sako ga Adamu, Omisore da sauran zababbun shugabanni

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci Sanata Adamu Abdullahi da ya duba cancanta sama da komai wajen zabar yan takara a zaben 2023
  • Shugaban kasar ya kuma bukaci mambobin APC da su ci gaba da hada kansu sannan su marawa sabon shugabancin jam;iyyar baya
  • Sanata Abdullahi ne ya zama sabon shugaban jam’iyyar mai mulki a taron da aka yi a ranar Asabar, 26 ga watan Maris

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci sabuwar zababbiyar uwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Sanata Adamu Abdullahi da ta tabbatar da ganin cewa wadanda suka cancanta ne suka mallaki tikitin jam’iyyar a zaben 2023.

Buhari ya bukaci sabbin shugabannin da su inganta damokradiyyar cikin gida da daidaito sannan su tabbatar da ganin cewa ba’a yi cuwa-cuwa ba a zaben fidda gwanin jam’iyyar gabannin zaben 2023, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar takara: APC za ta shirya fitar da jerin sunayen hadin kai na taron gangami

Gangamin taron APC: Buhari ya aika gagarumin sako ga Adamu, Omisore da sauran zababbun shugabanni
Gangamin taron APC: Buhari ya aika gagarumin sako ga Adamu, Omisore da sauran zababbun shugabanni Hoto: APC
Asali: Twitter

Da yake jawabi a babban taron gangamin jam’iyyar da aka yi a ranar Asabar, a Eagle Square Abuja, shugaban kasar ya kuma yi kira ga mambobin APC da su ci gaba da kasancewa a hade da karfi sannan su marawa sabon shugabancin jam’iyyar baya.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan taro na zuwa ne a lokaci mai muhimmanci lokacin da muke shirin wani babban zaben. Don haka, akwai mukatar mu ci gaba da kasancewa cike da kwarin gwiwa da hadin kai domin nasarar jam’iyyarmu.
“Mun yaba da ‘yancin rike ra’ayoyi da buri daban-daban, duk da haka, dole ne kada irin wannan bambance-bambancen ya cutar da Jam’iyyar.
“Ina mai rokonku a kan duk ku ba sabon kwamitin NWC goyon baya domin inganta hadin kai da guje ma wa tunanin da zai iya haifar da rashin jituwa da rashin hadin kai.

Kara karanta wannan

Mu ya mu: ‘Yan takarar shugaban kasa na PDP sun gana don zaban daya kwakkwara

“Ga wadanda ke takarar kujerun jam’iyyar, rashin cimma wannan kudiri naku kada ya zama dalilin da zai sa ku juyawa jam’iyyar baya.
“Ya kamata mu dauki dabi’ar yan wasan motsa jiki sannan mu dunga goyon bayan jam’iyyar a koda yaushe domin ta yi nasara.”

Ku Bani Kuɗi Kawai, Ba Kujerar Shugaban Ƙasa Na Ke So Ba, Amaechi Ya Faɗa Wa Magoya Bayansa

A wani labarin, ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yayin da ya ke karyata jita-jitar cewa zai fito takarar shugaban kasa a 2023, ya bukaci magoya bayansa su bashi kudi a maimakon kujerar shugabancin kasar.

Idan za a tuna, The Punch ta rahoto cewa wata kungiya, Amaechi Vanguard a Amurka da Canada, ta bukaci jam'iyyar na APC ta zabi Amaechi a matsayin dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa a 2023.

A bangarensa, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce zai iya yin takarar shugabancin kasa a 2023 ne, a matsayin shugaban kasa ko mataimaki tare da Amaechi, idan Shugaba Buhari ya dage kan hakan.

Kara karanta wannan

Lissafi ya canza: Shugaban kasa ya bada sabon umarni a kan zaben shugabannin jam’iyya

Asali: Legit.ng

Online view pixel