Ku Bani Kuɗi Kawai, Ba Kujerar Shugaban Ƙasa Na Ke So Ba, Amaechi Ya Faɗa Wa Magoya Bayansa

Ku Bani Kuɗi Kawai, Ba Kujerar Shugaban Ƙasa Na Ke So Ba, Amaechi Ya Faɗa Wa Magoya Bayansa

  • Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri (Dan Amanar Daura) ya shaida wa magoya bayansa cewa shi fa yanzu kudi kawai ya ke bukata domin ya kula da kansa
  • Ya yi wannan furucin ne yayin martani ga wasu kungiyoyin magoya bayansa da suka bukaci jam'iyyar mai mulki ta APC ta bashi tikitin takarar shugaban kasa a 2023
  • Duk da hakan, wasu rahotanni sun nuna cewa an hangi fastocin takarar shugabancin kasa na Amaechi a wurin taron gangamin APC da aka yi a ranar Asabar

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yayin da ya ke karyata jita-jitar cewa zai fito takarar shugaban kasa a 2023, ya bukaci magoya bayansa su bashi kudi a maimakon kujerar shugabancin kasar.

Idan za a tuna, The Punch ta rahoto cewa wata kungiya, Amaechi Vanguard a Amurka da Canada, ta bukaci jam'iyyar na APC ta zabi Amaechi a matsayin dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Abin Da Yasa Na Hallarci Taron Ƙaddamar Da Takarar Atiku Duk Da Cewa Nima Zan Yi Takarar, Peter Obi

Ku Bani Kuɗi Kawai, Ba Kujerar Shugaban Ƙasa Ba, Amaechi Ya Faɗa Wa Magoya Bayansa.
Ku Bani Kuɗi, Ba Kujerar Shugaban Ƙasa Ba, Amaechi Ga Magoya Bayansa. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

A bangarensa, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce zai iya yin takarar shugabancin kasa a 2023 ne, a matsayin shugaban kasa ko mataimaki tare da Amaechi, idan Shugaba Buhari ya dage kan hakan.

Kudi na ke bukata ba kujerar shugaban kasa ba, Amaechi

Amaechi, yayin martaninsa game da bukatar ya fito takarar, ya ce abin da ya ke bukata kawai shine kudi da zai kula da kansa ba shugabancin kasa ba.

Da ya ke magana a Arise TV, ya ce:

"Mutanen da ke son in yi takarar shugabancin kasa a 2023, su bani kudi kawai. Ina bukatar kudi domin in kula da kai na."

Amma, wasu rahotanni sun nuna cewa an ga hotunan takarar shugabancin kasa na Amaechi a wurare da dama a Eagles Square, inda aka yi taron gangamin jam'iyyar APC a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

A bangare guda, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel