Ana daf da zaben shugabannin APC, Buhari ya hadu Tinubu da wadanda suka kafa jam’iyya

Ana daf da zaben shugabannin APC, Buhari ya hadu Tinubu da wadanda suka kafa jam’iyya

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira wani taro da aka yi da iyayen jam’iyyarsa ta APC
  • Bola Tinubu, Bisi Akande, da Rochas Okorocha sun halarci liyafar da Buhari ya shirya a Aso Villa
  • Nasir El-Rufai, Aminu Masari da Mai Mala Buni su na cikin wadanda aka rufe kofa da su a dazu

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gayyaci manyan ‘yan siyasar da aka kafa jam’iyyar APC da su zuwa wajen wata liyafa a Aso Rock.

Jaridar Daily Trust ta ce Mai girma shugaban kasa ya kira wannan liyafa a yammacin Alhamis, 24 ga watan Maris 2022, a yayin da ake shirin zaben APC.

Kamar yadda mu ka ji labari, Muhammadu Buhari ya zauna da manyan jam’iyyarsa ta APC ne domin ya yi masu godiya kan gudumuwar da suke badawa.

Kara karanta wannan

Babu yadda gwamnonin APC suka iya, sun goyi bayan wanda Buhari ke so a zaben jam'iyya

Shugaban kasar ya ji dadin yadda masu ruwa da tsaki a tafiyar APC suka ba shi hadin-kai, kuma suka fahimci kokarin da gwamnatinsa ta ke yi a kan mulki.

An yi wannan zama ne da nufin a tabbatar da an toshe kafar samun baraka a wajen zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa da za a gudanar a gobe.

Shugaban APC na farko da amininsa watau Bola Tinubu sun halarci zaman. An hangi Ministocin tarayya biyu, Sanatoci uku da Gwamnoni hudu a wajen taron.

'Yan jam’iyyar APC
Iyayen APC tare da Shugaban kasa Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Su wanene aka gani a taron?

Wadanda aka yi wannan taro da su sun hada da Cif Bisi Akande; Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Dr. Ogbonnaya Onu, Rochas Okorocha, da Ibrahim Shekarau.

People Gazette ta ce Aliyu Magatakarda Wamako, Nasir El-Rufai, Aminu Masari, Rotimi Amaechi su na cikin wadanda aka yi muhimmin zaman da su.

Kara karanta wannan

Lissafi ya canza: Shugaban kasa ya bada sabon umarni a kan zaben shugabannin jam’iyya

Ragowar su ne sakataren gwamnati, Boss Mustapha da kuma shugaban rikon na APC, Mai Mala Buni.

Buhari ya zauna da manyan APC

Kafin ayi wannan zaman da ya kasance ta bayan labule, shugaba Buhari ya gana da gwamnonin APC da masu takarar kujerar shugaban jam’iyya na kasa.

Har ila yau, Buhari ya hadu da shugabannin majalisar tarayya a fadar Aso Rock duk a kan batun.

An hana Ministoci shiga zabe

An ji cewa duk wani Minista ko wanda yake rike da kujerar da Shugaban kasa ko wani mai mulki ya ba shi, bai da ta-cewa a zaben shugabannin jam’iyyar APC.

Sabuwar sanarwar da aka fitar dazu ta tabbatar da cewa masu mukamai a gwamnati sai dai su halarci gangamin APC a matsayin ‘yan kallo, ba masu zabe ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel