Babu yadda gwamnonin APC suka iya, sun goyi bayan wanda Buhari ke so a zaben jam'iyya

Babu yadda gwamnonin APC suka iya, sun goyi bayan wanda Buhari ke so a zaben jam'iyya

  • An yi wani muhimmin zama a game da yadda za a tunkari zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bijiro da maganar Abdullahi Adamu, babu wanda ya yi masa adawa
  • Gwamnonin APC sun yadda za su mara baya domin Sanata Adamu ya zama shugaban jam’iyyar

Abuja - A ranar Laraba, 23 ga watan Maris 2022, gwamnonin da suke mulki a karkashin jam’iyyar APC suka yi na’am da abin da shugaban kasa ya zo da shi.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa gwamnonin na jam’iyyar APC sun yarda su goyi bayan Sanata Abdullahi Adamu ya zama shugaban APC na kasa.

Tun tuni Muhammadu Buhari ya nuna cewa Abdullahi Adamu yake sha’awar ya rike jam’iyya. Wannan matakin ya nemi ya jawo sabani tsakanin ‘yan APC.

Kara karanta wannan

Yadda mutane kusan 200 za su goge raini wajen neman mukamai 22 a Jam’iyyar APC

A karshen zaman da aka yi na ranar Laraba a Aso Rock, jaridar ta ce an cin ma matsaya cewa gwamnoni za su ba Sanatan duk goyon bayan da ake bukata.

Abdullahi Adamu zai kara ne da Tanko Al-Makura; Sani Musa; Saliu Mustapha; Saidu Etsu; George Akume da kuma Abdulaziz Yari daga yankin Arewa ta yamma.

Yemi Osinbajo da gwamnoni 16 suka halarci wannan zaman da aka yi a fadar shugaban kasa.

Buhari
Jagororin APC a Aso Rock Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Gwamnoni sun bi umarni

Gwamnonin da aka rufe labule da su, su ne na Kebbi, Filato, Yobe, Ogun, Kaduna, Ekiti, Ebonyi, Neja, Jigawa, Imo, Kwara, Zamfara, Ogun, Nasarawa da Borno.

Wani gwamnan Arewa ya shaidawa manema labarai cewa babu wanda ya yi adawa ga Adamu da aka dauko maganar a wajen taron da shugaban kasa ya kira.

Kara karanta wannan

Kan gwamnoni da jiga-jigai ya yi kwari, sun shirya yakar ‘Yan takarar Buhari a zaben APC

Haka zalika an cin ma matsaya daya a kan wanda zai zama sabon sakataren jam’iyyar APC na kasa. An samu wata majiya da ta tabbatar da wannan labari.

Da yake yi wa manema labarai jawabin bayan taro a Abuja, shugaban kungiyar gwamnonin APC na kasa, Atiku Bagudu ya ce kan gwamnonin jam’iyya ya hadu.

Arise TV tace Gwamnonin da suka yi jawabi a madadin yankunansu a wajen taron su ne; Babagana Zulum, Badaru Abubakar, Dave Umahi da Kayode Fayemi.

Lissafi ya canza a APC

Bayan jam’iyya ta lakume miliyoyi a ‘yan kwanaki da bude saida fam, an ji Muhammadu Buhari ya haramtawa APC cin kudin ‘yan APC da suka fasa shiga takarar.

Sannan kuma ana saura kwanaki biyu ayi zabe, shugaban kasa ya ce gwamnonin APC su fito da wadanda za su rike sauran mukaman da suka rage a jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel