Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP

Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP

  • Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya bayyana cewa tsarin karba-karba ba shine hanyar da ya dace PDP ta zabi dan takararta ba gabannin 2023
  • Tambuwal a ranar Talata, 22 ga watan Maris, ya yi bayanin cewa yan siyasa ne suka kirkiri tsarin karba-karba a baya don magance wata matsala
  • Gwamnan na jihar Sokoto ya kara da cewa yan takarar shugaban kasa na PDP sun yarda cewa dole a saka amfanin yan Najeriya sama da komai

Niger - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya ziyarci tsoffin shugabannin kasa, Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar a gidajensu da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

Tambuwal wanda ya isa garin Minna da yammacin ranar Talata, 22 ga watan Maris, ya fara ganawa da Babangida a gidansa da ke Uphill, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdülaziz Yari

Ya yi ganawar sirri da shi na kimanin awa daya kafin ya tafi gidan Abdulsalam da ke makwabtaka da na IBB.

Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP
Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP Hoto: Sokoto fact
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya zanta da tsohon shugaban na kimanin mintuna talatin 30.

Da yake magana da manema labarai bayan taron, Tambuwal ya bayyana cewa ya zo Minna ne daga cikin tuntuba da yake na shirin takarar shugabancin kasa karkashin PDP.

Ya bayyana cewa ba lallai ne zaben 2023 ya ta'allaka a kan karba-karba ba, inda ya bukaci jam'iyyar adawar da ta mayar da hankali wajen lashe zabe maimakon bin shiyya.

Ya yi bayanin cewa karba-karba mataki ne da yan siyasa suka yi amfani da shi don magance wani lamari a wancan lokaci, wato 'June 12'.

Ya bukaci jam'iyyun siyasa da su guje ma bin shiyya-shiyya sannan su mikawa yan Najeriya yan takara don su yanke shawara kan wanda za su zaba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

Tambuwal ya ce:

"Karba-karba mataki ne na da gangan da yan siyasar kasar nan suka haifar don magance wani lamari, wato 'June 12'.
" Me yasa da muka ga barkewar korona, ba mu yiwa annobar amfani da maganin kanjamau ba? Mika mulki da aka yi a 1999 ya kasance domin magance wani lamari a kudu maso yamma.
"Ku koma ga tarihin damokradiyya a Najeriya. A 1979, NPN na da Shagari, NPP na da Azikiwe, UPN na da Cif Awolowi, GNPP na da Waziri Ibrahim sannan PRP na da Aminu Kano.
"Babu tsarin karba-karba. Idan ka koma ga 1992/1993, SDP na da Abiola, NRC na da Bashir Tofa, babu karba-karba.
"Wannan na nuna maku cewa idan kuka koma ga tarihi, za ku gane cewa tsarin karba-karba ba shine babban matsalar ba.
"Babban al'amarin shine cewa jam'iyyun siyasa su ba yan takara dama sannan yan Najeriya su yanke shawara kan wanda za su zaba a matsayin shugaban kasar su."

Kara karanta wannan

Idan PDP ta ba dan kudu tikitin shugaban kasa, ba zamuyi nasara ba: Tambuwal

Gwamnan ya kara da cewar shi da sauran yan takarar jam’iyyar suna tattaunawa a tsakaninsu domin cimma matsaya daya.

Ya bayyana cewa akwai ci ci gaba a shirin gyara Najeriya tsakanin yan takarar jam’iyyar adawar.

Tambuwal: Zamu zauna da Atiku domin duba yuwuwar sulhu wajen tsayar da ɗan takara a 2023

A wani labarin, dan takarar shugaban ƙasa kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya ce zai tattauna da Atiku Abubakar domin duba yuwuwar fitar ɗan takarar PDP ta hanyar sulhu.

Gwamna Tambuwal ya faɗi haka ne yayin da yake hira a cikin wani shiri na kafar watsa labarai, Channels TV ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel