Idan PDP ta ba dan kudu tikitin shugaban kasa, ba zamuyi nasara ba: Tambuwal

Idan PDP ta ba dan kudu tikitin shugaban kasa, ba zamuyi nasara ba: Tambuwal

  • Daya daga cikin masu niyyar takarar kujeran shugaban kasa a 2023 ya bayyana dalilinsa na ganin tsarin kama-kama ba zai yiwa PDP kyau ba
  • Aminu Tambuwal wanda yayi takara a zaben 2019 na shirin sake takara a zaben 2023
  • Tambuwal yace a yanzu PDP nasara take bukata ba tsarin kama-kama ba saboda haka APC tayi a baya

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya bayyana cewa idan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta baiwa dan kudu tikitin takara a zaben 2023, da kamar wuya ayi nasara.

Tambuwal ya bayyana hakan yayin jawabi lokacin ganawarsa da tsaffin shugabannin majalisar dokokin tarayya ranar Talata, 22 ga Maris, 2022 a Abuja, rahoton Daily Trust.

A cewarsa, yana baiwa PDP da masu ruwa da tsaki shawarar su mayar da hankali kan lashe zaben tukun.

Kara karanta wannan

2023: Ku tsayar dani takarar shugaban kasa zan lallasa kowa a zabe, Gwamnan Arewa ya roki PDP

Tambuwal
Idan PDP ta ba dan kudu tikitin shugaban kasa, ba zamuyi nasara ba: Tambuwal Hoto: Aminu Waziri
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya yi wasu bayanai kan zabukan da akayi baya-bayan nan wanda a cewarsa zai yi wuya dan kudu ya lashe zaben shugaban kasa karkashin PDP.

Ya ce su tuna cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta baiwa dan jihar Katsina tikitin takara a 2015 duk da cewa marigayi Umaru Musa Yar'adua da ya mutu a mulki dan jihar Katsina ne.

Tambuwal ya ce jam'iyyar ta mayar da hankali kan nasara a zabe, sabanin tsarin kama-kama.

2023: Ku bani tikitin shugaban ƙasa zan kwato mana mulki, Gwamnan Arewa ya roki PDP

Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, ya roki jam'iyya ta duba yiwuwar tsayar da shi takara a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Tambuwal ya ce matukar PDP ta ba shi tikitin takara to zai share mata hawaye ya dawo mata karagar mulkin Najeriya, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Idan yan Najeriya suka zabeni, yan kasa da shekaru 35 zan nada Ministoci: Saraki

A cewar gwamnan jihar Arewa da zaran ya zama shugaban kasa zai ɗakko mambobin jam'iyya ya naɗa su manyan mukamai.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban mai taimaka masa ta ɓangaren yaɗa labarai, Muhammad Bello, kuma aka raba wa manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel