Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

  • Atiku Abubakar ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke son ganin ya mulke su a nan da 2023 mai zuwa
  • Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi dashi a kafar yada labarai ta BBC, inda ya yi maganganu da yawa
  • Daga ciki, ya bayyana cewa, burin 'yan Najeriya yake son cikawa na zama shugabansu, ba wai son ransa ba

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abukabar ya bayyana cewa yan Najeriya ne suka nemi ya tsaya takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, 22 ga watan Maris, kwana guda kafin ya ayyana takararsa a hukumance.

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku
Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku | Hoto: dailytrust.com
Asali: Depositphotos

Atiku ya kuma ce zai yi takara ne saboda kawo wa alumman kasar sauki kan matsalolin da suke fuskanta.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

Da aka tambaye shi kan yadda zai yi da sauran abokanan takararsa na PDP, sai Atiku ya ce ba su da wata matsala a jam'iyyar domin kuwa idan suka zauna za su fitar da dan takara cikin ruwan sanyi.

Ya ci gaba da shaidawa BBC Hausa cewa::

"Makasudin tsayawana takara shine domin akwai abin da ban taba gani ba a rayuwana a kasar. Na daya shine rashin hadin kan kasar nan musamman a bangarori daban-daban. Na biyu akwai rashin zaman lafiya. Na uku tattalin arzikin kasar nan ya wargaje gaba daya.
"Baya ga haka, an samu koma baya a fanni daban-daban na yan adam a kasar nan."
"To wadannan kuma tunda shike magoya bayana wadanda suna da dama, wadansu suna cikin jam'iyyu daban-daban ba wai sai a jam'iyyar PDP kawai ba, suka ce ya kamata na sake fitowa na ba yan kasar nan shugabanci irin shugabanci da muka bata tsakanin 1989 zuwa 2007."

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Akwai matsaloli a Najeriya

Game da abin da yake ganin ya kawo matsalar Najeriya, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:

"Ba shakka akwai matsaloli kwarai da gaske na rashin zaman lafiya kuma wadannan abhbuwa sun faru ne don rashin shugabanci."

Kan fatarsa game da Najeriya, sai ya ce:

"Fatana shine mu tabbatar da mun fitar da Najeriya cikin kangin nan da muka samu kanmu yanzu na koma baya musamman tattalin arzikin kasa da rashin aikin yi, da rashin zaman lafiya da kuma rarraba kawunan mutane da aka yi."

2023: Shugabannin PDP Na Kudu Sun Yi Taro, Sun Ce Dole Shugaban Kasa Ya Fito Daga Yankinsu

A wani labarin, jiga-jigan jam'iyyar PDP na Kudu maso Yamma su yi taro a ranar Talata, inda suka yanke shawarar cewa daga yankin kudu ya kamata jam'iyyar ta fitar dan takarar shugaban kasa.

Wanann na daga cikin batutuwan da aka amince a kansu a karshen taron na jiga-jigan jam'iyyar PDP reshen Kudu maso Yamma da aka yi a gidan gwamnati, Agodi, Ibadan, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ministan shari'a Malami: Ba zan yi murabus ba, sai na kammala wa'adin aiki na a mutunce

Shugaban jam'iyyar PDP na yankin kudu maso yamma, Cif Soji Adagunodo, ya karanta sakon bayan taro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel