Ku samar da sashin harkokin siyasa don tallata yan uwanku Musulmai, Tinubu ga shugabannin Musulunci

Ku samar da sashin harkokin siyasa don tallata yan uwanku Musulmai, Tinubu ga shugabannin Musulunci

  • Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ya bukaci majalisar koli ta addinin Musulunci da ta samar da wani sashi na harkokin addini
  • Tinubu ya ce ta hankan ne majalisar za ta wayar da kan mabiyanta domin tallata yan uwansu da ke neman shugabanci
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas dai na neman darewa kujerar shugaban kasa a zaben 2023

Osun - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya bukaci majalisar koli ta shari’a ta kasa da ta kafa wani sashi na harkokin siyasa domin wayar da kan mabiya addinin game da samar da shugaban kasa Musulmi a zaben 2023.

Da yake magana a taron kafin Ramadan na kungiyar ta SCSN, wanda aka gudanar a Osogbo, babban birnin jihar Osun, Tinubu ya ce Musulmai ba za su yarda a barsu a baya ba wajen shiga harkokin siyasar kasar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bode George: Zan tattara na koma Ghana sannan na dunga kallo daga nesa idan Tinubu ya zama shugaban kasa

Ku samar da sashin harkokin siyasa, Tinubu ya bukaci shugabannin addinin Musulunci
Ku samar da sashin harkokin siyasa, Tinubu ya bukaci shugabannin addinin Musulunci Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Yayin da yake neman goyon bayan kungiyar don cimma kudirinsa na son zama shugaban kasa, Tinubu, wanda ya samu wakilcin Asiwaju Musulumi na jihohin Yarbawa, Edo da Delta, Cif Tunde Badmus ya jaddada bukatar ganin Musulmai sun shiga lamuran siyasar kasar kamar sauran kungiyoyi.

Ya kara da cewa:

“Sauran kungiyoyin addinai sun fara wayar da kan mabiyansu kan harkokin siyasa ta hanyar kirkirar kungiyoyi a tsakaninsu don tallata nasu. Ya kamata ku kirkiri wani sashi na siyasa a tsakaninku domin karfafa shigarku siyasa, zai kasance kafa mai kyau don marawa yan uwan da ke neman mukaman siyasa baya.
“Akwai bukatar mu jajirce wajen addu’o’in samun shugaba nagari amma akwai bukatar mu shiga harkokin siyasa. Allah na amsa addu’o’inmu ne ta abubuwan da muke yi, don haka yayin da muke addu’a, toh mu yi aiki a kai."

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Tinubu ya bayyana cewa zai ziyarci kungiyar a fadin kasar don samun goyon bayanta wajen cimma kudirinsa na son zama shugaban kasa, yana mai cewa:

“Ta hannun shugaban majalisar shari’ar a Najeriya, zan ziyarci duk jihohin kasar nan. Ba zan iya samun damar ganin daukacin Musulman Najeriya ba amma ta shugabannin Musulunci, za mu iya cimma haka.”

Da yake jawabi ga manema labarai, babban sakataren kungiyar, Sheikh Nafiu Baba Ahmed, ya ce an yi taron ne da nufin saita ajandar wa’azin malamai a watan Ramadan wajen karfafawa al’umma gwiwar shiga a dama da su a harkar siyasa, rahoton Sahara Reporters.

Bode George: Zan tattara na koma Ghana sannan na dunga kallo daga nesa idan Tinubu ya zama shugaban kasa

A gefe guda, jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bode George, ya bayyana cewa zai tattara ya koma kasar Ghana idan tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Tinubu, ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace

Tinubu, wanda ya kasance babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya sanar da aniyarsa ta son yin takarar shugaban kasa a babban zaben kasar mai zuwa.

Tun bayan lokacin, tsohon gwamnan na jihar Lagas da magoya bayansu sun zagaya yankuna da daman a kasar domin tattaunawa da sarakuna da masu ruwa da tsaki a harkar siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel