Jam'iyyar APC ta bayyana yan majalisu 14 da zata baiwa tikitin takara kai tsaye a 2023

Jam'iyyar APC ta bayyana yan majalisu 14 da zata baiwa tikitin takara kai tsaye a 2023

  • Gabanin zaben 2023 dake tafe, jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta fara shirye-shiryen kawar da PDP daga mulkin jihar
  • Duk da sauya shekar gwamna mai ci zuwa tsagin hamayya PDP, cikin kwarin guiwa APC tace zata lashe kujerun yan majalisu baki daya
  • Gwamna Godwin Obaseki wanda ya raba gari da APC tun bayan sauya shekarsa, zai sha mamaki a zaben 2023 inji APC

Edo - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Edo, ta ce zata damƙa wa yan majalisu 14 tikitin takara kai tsaye ba tare da hamayya ba a zaɓen 2023, kamar yadda The Nation ta rahoto.

A cewar Sakataren APC na jihar Edo, Lawrence Okah, waɗan nan yan majalisu sun haɗa da waɗan da suka ci nasara a babban zaɓen da ya shuɗe na 2019.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna ya fice daga APC, ya bi sahun Kwankwaso zuwa NNPP

Mista Okah, ya yi wannan furucin ne ranar Talata, 15 ga watan Maris, 2022 a Benin, yayin sanar da Osaro Obazee a matsayin dan takarar kujerar mazaɓar Oredo, a majalisar tarayya.

Tutar APC
Jam'iyyar APC ta bayyana yan majalisu 14 da zata baiwa tikitin takara kai tsaye a 2023 Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Yayin da yake jawabi ga mambobin jam'iyya, Sakataren APC ya bayyana cewa dalili ɗaya da zai hana ɗan takara ya samu tikiti kai tssaye shi ne idan shi ne baya so.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa duk ɗan takarar da baya so, to jam'iyya ba zata tursasa shi ba, a cewar Sakataren.

Haka nan kuma ya yaba wa Obazee bisa nasarorin da ya cimma wa a jihar da kuma mazaɓarsa. Mista Okah ya ce:

"Osaro Obazee ya yi abin a yaba, ya zama abin alfaharin garin nan. Wannan wani darasi ne da mutane zasu gane cewa kishin ƙasa yana da matukar alfanu. Mun san abin da ya yi lokacin yana Ciyaman a Oredo."

Kara karanta wannan

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

APC ta jinjina wa gwarazan yan majalisu

Kazalika a jawabinsa, Sakataren APC ya jinjina wa yan majalisun jihar Edo 14 bisa tsantsar ƙaunar da suka nuna wa jam'iyya da sadaukarwan da suka yi ga manufofinta.

Duk da sauya shekar gwamna mai ci, Okah ya gode musu bisa tsaida duga-duginsu da gyara zama a cikin jam'iyyar APC.

A nasa jawabin, Obazee ya ce ya na neman sake komawa majalisa ne saboda sadaukarwar da ya yi wa mazaɓarsa kuma a acewarsa ya na da kwarin guiwar sake lashe zaɓe.

Ya ce:

"Zan lashe zabe matuƙar APC ta sake bani tikiti, ni ke ba da shawara a harkokin siyasar karamar hukumar Oredo. Ba wai ina yabon kai na bane, amma ba na tsoro, matukar na sami tikitin APC zan gwabza a gwamnati mai ci."

A wani labarin na daban kuma Ɗiyar Bola Tinubu ta yi tsokaci kan shirin mahaifinta na gaje kujerar Buhari

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗiyar Bola Tinubu ta yi tsokaci kan shirin mahaifinta na gaje kujerar Buhari

Ɗiyar Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa mahaifinta ya shirya tsaf domin jan ragamar mulkin Najeriya a 2023.

Tinubu-Ojo, ta ce kowane abu kan samu matsala kuma ya warware, kamar haka ne mahaifinta ya yi rashin lafiya kuma ya warke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel