Tsohon mataimakin gwamna ya fice daga APC, ya bi sahun Kwankwaso zuwa NNPP

Tsohon mataimakin gwamna ya fice daga APC, ya bi sahun Kwankwaso zuwa NNPP

  • Tsohon Mataimakin gwamna a Adamawa, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa NNPP mai kayan marmari
  • Sa'ad Tahir, ya koma jam'i'iyyar APC a 2018 domin ba da gudummuwarsa, yanzu kuma ya koma NNPP don kara wa demokaradiyya karfi
  • A wani cigaban, tsohon ciyaman na ƙaramar hukumar Madagali, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Adamawa - Tsohon mataimakin gwamna a jihar Adamawa, Sa'ad Tahir, ya fice daga jam'iyyar APC, ya koma jam'iyyar NNPP da ake ganin Kwankwaso zai koma.

Tahir ya sanar da batun sauya shekarsa ne a wani taron Manema labarai ranar Talata a Yola, babban birnin Adamawa, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Idan baku manta ba a shekarar 2014, Alkalin babbar Kotun tarayya dake zaune a Abuja ya bada umarnin tsige mukaddashin gwamna, Ahmadu Fintiri na Adamawa tare da maye gurbinsa da Bala Ngilari.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana yan majalisu 14 da zata baiwa tikitin takara kai tsaye a 2023

Jam'iyyar NNPP
Tsohon mataimakin gwamna ya fice daga APC, ya bi sahun Kwankwaso zuwa NNPP Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A wannan lokacin aka zabi Tahir a matsayin mataimakin gwamna ga Bala Ngilari ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

A watan Disamba, 2018, tsohon mataimakin gwamnan ya watsar da PDP, ya koma jam'iyyar APC, kuma ya cigaba da zama a jam'iyyar har zuwa yanzu da aka samu cigaba.

Yace ɗaya ɗaga cikin dalilansa na sauya sheka a wannan lokaci shi ne domin ya samu cikakkiyar dama ta kare martabar Demokaraɗiyya.

Ya ce:

"A shekarar 2018 na bar PDP zuwa APC ne domin ƙara wa demokaradiyyar mu ƙarfi."

APC ta yi babban kamu

A wani cigaba mai kama da wannan, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Madagali, Chubado Tijjani, wan da ya shafe zango biyu ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Da take martani kan lamarin, jam'iyyar PDP ta bayyana sauya shekarsa a matsayin, "samun sauki ga jam'iyya."

Kara karanta wannan

Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace

Shugaban PDP na gundumar Madagali, Abdu Jabu, ya ce jam'iyya ba ta taba ɗaukar Tijjani a matsayin cikakken ɗan jam'iyya.

A wani labarin kuma ɗan majalisa da Shugabannin APC na tsagin Ministan Buhari sun sauya sheƙa daga jam'iyyar APC

Wasu shugabannin APC na tsagin ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, sun tabbatar da ficewarsu daga APC.

Sakataren kuɗi na tsagin, Tajuddeen Mohammed, ya ce a halin yanzun ba su yanke jam'iyyar da zasu koma ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel