Gwamnan APC ya canza magana, ya ce har yanzun Mala Buni ne shugaban APC na ƙasa

Gwamnan APC ya canza magana, ya ce har yanzun Mala Buni ne shugaban APC na ƙasa

  • Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce duk san da Buni ya dawo zai karbi jagorancin jam'iyyar APC ta ƙasa
  • Gwamnan wanda ke cikin gwamnonin da suka juya wa Buni baya, ya ce dole sai an bi matakai kafin tsige Mala Buni
  • Jam'iyyar APC ta shiga rikici ne tun bayan tafiyar Buni Dubai duba lafiya da kuma ganin gwamnan Neja ya maye gurbinsa

Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, yace har yanzu takwaransa na jihar Yobe, Mala Buni, ne shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa.

Kujerar Buni ta shiga rububi a makon da ya gabata, bayan gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya karbi jagorancin jam'iyya.

Gwamna Bello ya maye gurbin shugaban jam'iyya ne bayan gwamna Buni ya tafi Dubai a duba lafiyarsa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta yi amai ta lashe, tace har yanzu Gwamna Mala Buni ne shugabanta

Gewamnan Imo, Hope Uzodinma
Gwamnan APC ya canza magana, ya ce hara yanzun Mala Buni ne shugaban APC na ƙasa Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Shugaba Buhari na bayan Bello ya maye gurbin kujerar shugaban riko, a cewar gwamna Malam El-Rufa'i, na jihar Kaduna, yayin da ake raɗe-raɗin Buni na shirin ƙara jan babban taro na ƙasa a wannan watan.

Shin har yanzun suna shirin tsige Buni?

Da yake zantawa da Channels tv a cikin shirin 'Siyasa a Yau' ranar Litinin, Uzodinma ya ce dole sai an bi matakai kafin a cire Buni daga kujerarsa.

Gwamnan ya ce:

"APC jam'iyya ce mai hankali da nutsuwa, duk abin da ke wakana a Sakatariya gwamna Buni na sane da komai. Kuma da zaran ya dawo zai koma kan kujerarsa."

Matukar ana son canza Mala Buni, to wajibi ne a kira taron majalisar koli ta jam'iyyar APC, a cewar Uzodinma.

Kara karanta wannan

Tsige Mala Buni: Gwamnoni 2 da Minista sun garzaya Landan, za su sa labule da Buhari

"Ɓangaren jam'iyya da yake da ikon yanke hukuncin canza shugaba shi ne kwamitin zartarwa na jam'iyya. Shin mun kira taron wannan kwamiti?"
"Saboda duk randa muka kira wannan taron dole mu gayyaci INEC ta sa ido, idan hukumar ta halarta to duk abinda muka zartar za su ɗauka."

A wani labarin na daban kuma kan Takara a 2023, Kwamishinoni biyu sun yi murabus daga mukamansu a jiha daya

Yayin da guguwar siyasar 2023 ke cigaba da kaɗawa, Mutum biyu daga majalisar kwamishinonin Akwa Ibom sun yi murabus.

Kwamishinan cigaban tattalin arziki da tashar jiragen ruwa, ya mika godiyarsa bisa damar aiki da gwamna Emmanuel ya ba shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel