Da Dumi-Dumi: Wike ya maida wa Obaseki Martani mai zafi, yace gwamnan ma ci amana ne

Da Dumi-Dumi: Wike ya maida wa Obaseki Martani mai zafi, yace gwamnan ma ci amana ne

  • Rikici tsakanin gwamnonin jam'iyyar PDP biyu ya kara tsananta, Wike ya kara mauda wa Obaseki martani mai zafi
  • Wike ya roki tsohon shugaban APC na ƙasa gafara bisa kin ɗaukar gargaɗinsa game da halayen gwamna Obaseki na Edo
  • Gwamnan ya ce shi ba ajin Obaseki bane a jam'iyyar PDP kuma abin da ya yi wa jam'iyya ko kafarsa ba zai kamo ba

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ɗau zafi game da takwaransa na jihar Edo, Godwin Obaseki, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamna Wike ya bayyana gwamnan Edo da babban ma ci amana kuma mutum mara godiyar Allah.

Wike, wanda ya ƙaryata ikirarin gwamna Obaseki da ya yi a kansa, ya ce ko tsohon ubangidan gwamnan Edo kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, ya wanku sarai daga tuhuma.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Matar Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a cikin kotu

Wike da Obaseki
Da Dumi-Dumi: Wike ya maida wa Obaseki Martani mai zafi, yace gwamnan ma ci amana ne Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wike ya mika kokon baran neman afuwa ga Kwamaret Oshionhole bisa watsi da gargaɗin da ya masa game da Obaseki a baya.

Ya kara da cewa duk abin da tsohon shugaban jam'iyyar APC ya faɗa game da halayen Obaseki duk sun fito fili kowa ya gani.

Punch ta rahoto a kalaman gwamna Wike ya ce:

"Duk wanda ka tambaya ko ka duba jinin gwamna Obaseki, zaka gano shi babban ma ci amana ne kuma mutum mara godiyar Allah."
"Ina rokon Kwamaret Oshiomhole ya yafe mun domin ya faɗa mana komai game da Obaseki. Ya wanku sarai daga zargin da ake masa."

Nafi karfin ajin ka a PDP - Wike

Da yake jawabi a wurin buɗe makarantar Sakandiren al'umma Omuanwa, a jihar Rivers, Wike ya yi ikirarin cewa ya kawo wa PDP nasara fiye da Gwamna Obaseki.

Kara karanta wannan

Rikici ya kara tsanani tsakanin gwamnonin PDP, sun fara nuna wa juna yatsa

Ya ce:

"Ni ba ajin Obaseki bane kuma ba ɗaya muke ba, na fi karfinsa ba zamu taba zamo wa ɗaya ba. Ni ne Darakta Janar na yaƙin neman zaɓe, na je har Edo na shafe kwanaki uku."
"Na kai gwauro na kai mari ba tare da na yi wanka ba, bantaɓa ganin mutum kamar haka ba, babban ma ci amana. Bari na faɗa maka Obaseki, na san ire-iren ku, kuma zan maganin ku."
"Obaseki, na bauta wa PDP fiye da kai. Na yi wa jam'iyya yaƙi. Ka faɗa mun abu ɗaya da ka taɓa yi wa jam'iyyar PDP na a zo a gani."

A wani labari na daban kuma Manyan kayan abinci uku da farashin su ya yi tashin gwauron zabi a kasuwar Legas

Farashin kayayakin masarufi a kasuwar jihar Legas na sama suna ƙasa saboda kalubalen tsaro, canjin kudi da sauran su.

Karancin Man fetur ba ya cikin abubuwan da suka jawo tashin kayan, sai dai yan kasuwa sun ce rashin dai-daiton tattalin arziki ne babban dalili.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Ban Nemi Mulki Ba, Mulki Ne Ta Riƙa Bi Na A Guje

Asali: Legit.ng

Online view pixel