‘Yan siyasa 6 da za su iya bayyana shirin takarar shugaban kasa nan da kwanaki masu zuwa

‘Yan siyasa 6 da za su iya bayyana shirin takarar shugaban kasa nan da kwanaki masu zuwa

  • Kawo yanzu jiga-jigan ‘yan siyasa sun fara fito da niyyarsu ta tsayawa takara a zaben 2023 a fili
  • Bola Tinubu ya bude kofa a farkon 2022, ya ce zai nemi takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa
  • Har zuwa yanzu akwai manyan ‘yan siyasan da ba su ce uffan a game da neman shugabanci ba

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta kawo jerin wadannan ‘yan siyasa da nan da wasu ‘yan kwanaki kadan ake sa ran za su bayyana niyyarsu ga Duniya.

Su wanene wadannan ‘yan siyasa?:

Osinbajo zai tsaya takara?

1. Yemi Osinbajo

Daga cikin wannan jeri akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo wanda aka ji cewa ya sanar da Muhammadu Buhari burinsa na neman mulki.

Da zarar abubuwa sun kankama, Legit.ng Hausa ta na ganin cewa Osinbajo zai sanar da ‘Yan Najeriya shirin tsayawa takarar shugaban kasa a karkasin APC.

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Atiku Abubakar

Tun tuni ake sa ran Atiku Abubakar zai fito fili ya bayyana niyyarsa na neman mulki. Mun fahimci cewa nan da karshen Maris zai shiga neman tikitin PDP da gaske.

Magoya-baya su na cigaba da zagaye fadin kasar nan domin taya shi yakin neman zabe. A saurari tsohon mataimakin shugaban kasar da zarar PDP ta tsaida masaya kan 2023.

‘Yan siyasa
Secondus, Atiku, Saraki, Kwankwaso a Kano Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

3. Bukola Saraki

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya fito yana cewa zai iya rike shugabancin kasar nan. Hakan ya nuna zai sake jarraba sa’arsa a 2023.

Ko da Saraki bai ayyana shirin takara ba, magoya baya su na cigaba da yi masa aiki. Tsohon gwamnan na Kwara ya dade ya na neman tikitin takarar shugaban kasa.

4. Chris Ngige

Rahotanni da-dama su na nuni ga cewa Sanata Chris Ngige zai nemi a ba shi tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da yasa ban bayyana sha'awar gaje Buhari ba a hukumance, Bukola saraki

Tun kwanaki wasu ‘yan jam'iyyar APC na reshen jihar Anambra su ka bukaci Ministan kwadago ya yi takara. Hakan na nufin dole Ministan zai ajiye aiki kwanan nan.

5. Rotimi Amaechi

Wani Minista mai-ci a gwamnatin Muhammadu Buhari da ake hasashen zai nemi kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa shi ne Hon. Rotimi Chibukwe Amaechi.

‘Dan Amanan Daura yana da fada wajen shugaban kasa wanda shi ne ya yi masa Sarkin yakin zabe a 2015. Za a san matsayar tsohon gwamnan na Ribas kwanan nan.

6. Rabiu Kwankwaso

Bisa dukkan alamu tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai bayyana niyyar takarar shugaban kasa a zaben 2023 da zarar ya fice daga PDP.

A halin yanzu kafar tsohon Ministan ta shiga jam’iyyar adawa ta NNPP. Ana tunanin da zarar Kwankwaso ya bada sanarwar shiga NNPP, zai ayyana shirin yin takara.

PDP za tayi zama

A ranar Talatar nan ne ake sa ran cewa shugabannin majalisar NEC na jam’iyyar PDP za su yi wani muhimmin taro domin a tsaida inda za a kai takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

A karshe, Osinbajo ya zauna da Buhari a kan shirin takarar shugaban kasa a zaben 2023

A karshen taron ne za a san daga ina ‘dan takarar PDP a zaben shugaban kasa zai fito. Daga bisani za a kai matsayar da aka cin ma gaban majalisar BOT da kuma gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel