APC ta gamu da gagarumin cikas a wata jihar kudu yayin da kansiloli 5 suka fice, sun koma PDP

APC ta gamu da gagarumin cikas a wata jihar kudu yayin da kansiloli 5 suka fice, sun koma PDP

  • Gabannin babban taronta na kasa, wasu mambobin APC a Cross River sun fice daga jam’iyyar
  • Bayan ficewar tasu daga jam'iyya mai mulki, sai suka koma jam’iyyar PDP mai adawa
  • An gabatar da kansilolin su biyar a gaban mai neman takarar gwamnan jihar a zaben 2023

Cross River - Wasu yan majalisar karamar hukumar Obanliku a jihar Cross River su biyar sun sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Labarin sauya shekar kansilolin biyar ya bayyana ne a karshen mako lokacin da aka gabatar da su a gaban mai neman takarar gwamna na PDP a jihar, Sanata Gershom Bassey, Thisday ta rahoto.

APC ta gamu da gagarumin cikas a wata jihar kudu yayin da kansiloli 5 suka fice, sun koma PDP
APC ta gamu da gagarumin cikas a wata jihar kudu yayin da kansiloli 5 suka fice, sun koma PDP Hoto: Joseph Duke
Asali: Facebook

Kansilolin wadanda shugaban PDP a karamar hukumar Obanliku, Hon. Justine Ejisekpe, ya gabatar da su a gaban mai neman takarar gwamnan sune, Hon. Adida Justin, Hon. Ololo Francis, Hon. Helen Ejikang, Hon. Ogor Doris da Hon. Polycarp Ugiugbong.

Kara karanta wannan

Yadda Mai Mala Buni da shugabannin APC suke fama da shari’a fiye da 200 a gaban kotu

Da yake jawabi ga Sanata Bassey da mukarrabansa, Ejisekpe, ya ce kansilolin sun dawo jam’iyyar PDP, kuma za su baiwa jam’iyyar goyon bayan da ya dace domin ganin ta lashe zaben 2023 a yankunansu da ma jihar baki daya.

Shugaban PDPn wanda ya ce Bassey na da kirki, saukin kai da kuma kishin kasa ya bayyana cewa yana da kyawawan halayya na shugaban da ke muradn kawo sauyi ga al’ummansa.

Ya roki mai neman takarar gwamnan da ya tuna da matasan Obanliku wadanda basu da aiki sannan ya taimaka masu idan ya zama gwamnan jihar, rahoton Thisday.

Kansilolin sun kuma nuna gagarumin goyon baya ga takarar Bassey sannan su bashi tabbacin nuna cikakken biyayyarsu gare shi da PDP.

Bukola Saraki ya bayar da gagarumin shawara ga ministocin Buhari

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi babban Kamu, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPP

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, ya yi kirfa ga masu rike da mukamai da ke neman yin takara a zaben 2023 da su yi murabus daga mukamansu na ministoci kafin su fara neman cimma burinsu.

Saraki ya kuma soki bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dokokin kasar inda ya nemi a gyara sashi 84 (12) na dokar zabe.

Sashin ya haramtawa masu rike da mukaman siyasa yin zabe ko kuma a zabe su a yayin tarurrukan jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel