Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamna Da Mataimakinsa Saboda Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamna Da Mataimakinsa Saboda Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC

  • Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da mataimakinsa Kelechi Igwe sun rasa kujerunsu saboda ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Kotun ta yanke hukuncin cewa kuri'un da suka samu yayin zaben gwamna na jam'iyyar PDP ne don haka Umahi da mataimakinsa sun rasa kuri'un bayan ficewarsu daga jam'iyyar
  • Kotun ta umurci INEC ta karbi zabin sunayen wadanda za su maye gurbin Umahi da mataimakinsa daga PDP ko kuma ta sake sabon zaben gwamna a jihar

FCT, Abuja - Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, a kori Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da Mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe, bayan sun fice daga jam'iyyar PDP sun koma APC mai mulkin sa, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ba na shirin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, Mataimakin gwamna ya magantu

Kotun, a hukuncin da Mai sharia Inyang Ekwo, ya yi, ta ce kuri'u 393,042 da Gwamna Umahi ya samu a zaben ranar 6 ga watan Maris na gwamnan Jihar Ebonyi, na jam'iyyar PDP ne kuma doka bata amince a mayarwa APC ba.

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamna Da Mataimakinsa Saboda Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC
Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamna Umahi Da Mataimakinsa Saboda Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

A cewar kotun, bayan komawa jam'iyyar APC, Umahi da mataimakinsa, ba PDP kadai suka bari ba, sun raba kansu da kuri'un jam'iyyar ta PDP, Daily Trust ta rahoto.

Kotun ta ce idan aka yi la'akari da sakamakon zaben na gwamna, kujerar gwamnan Jihar Ebonyi da mataimakinsa, 'mallakar wanda suka yi karar ne ba wata jam'iyyar daban ba.'

"Babu wani tanadi a kundin tsarin mulkin kasa da ya nuna ana iya musayar kuri'u daga jam'iyya daya zuwa wata jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Ta ce jam'iyyar PDP ce ke da kuri'un da kujerun da masu zabe a Jihar Ebonyi suka kada, don haka ba za a iya mika wa Gwamna Umahi da mataimkinsa kuri'un ba idan sun fice daga jam'iyyar.

Don haka kotun ta bada umurnin cewa nan take Dave Umahi da Igwe su ajiye mukamansu.

Kotu ta umurci INEC ta karbi sunayen wadanda za su maye Umahi da mataimakinsa daga PDP ko ta sake sabon zabe

Ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta karbi sunayen mutanen da za su maye gurbin Umahi da mataimakinsa daga PDP, ko kuma ta sake yin sabon zabe a jihar Ebonyi kamar yadda sashi na 177(c) na kundin tsarin mulki da aka yi wa kwaskwarima ya ce.

Kotun ta kuma hana Umahi da mataimakinsa Igwe cigaba da amsa sunan gwamna da mataimakinsa na jihar Ebonyi.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan karar da jam'iyyar PDP ta shigar bayan Umahi da mataimakinsa sun koma APC.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jami'an tsaro sun mamaye sakateriyar APC ta kasa dake Abuja

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

A wani labarin, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel