Ba na shirin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, Mataimakin gwamna ya magantu

Ba na shirin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, Mataimakin gwamna ya magantu

  • Mataimakin gwamna Obaseki na Edo ya ce ba ya shirin fita daga PDP zuwa APC amma dai ba'a nuna musu kauna a PDP
  • Philip Shaibu ya ce da yawan magoya bayan gwamna sun gaji da abin da ake musu a PDP, shiyasa suke tunanin canza sheka
  • A cewarsa sun bar APC a wancan lokaci ne ba wai don suna kaunar shiga PDP ba, sai dan kare mutuncin gwamnan su

Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, a ranar Litinin, ya ce sabanin raɗe-raɗin da ake yaɗawa, ba zai fice daga PDP ya koma APC ba.

Channels tv ta rahoto cewa bayan samun matsala da tsohon ubangidansa, Adams Oshiomhole, bisa tilas Shaibu da kuma maigidansa gwamna Obaseki suka fice daga APC, suka koma PDP.

Kara karanta wannan

Babu maganar janye yajin-aiki, kungiyar ASUU ta gindayawa Gwamnatin Najeriya sharadi

Mutanen biyu sun samu tikicin takara a PDP kuma suka zarce wa'adi na biyu bayan ayyana su a matsayin waɗan da suka lashe zaɓen watan Satumba, 2020.

Mataimakin gwamna Edo. Philips shaibu
Ba na shirin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, Mataimakin gwamna ya magantu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kusan shekara biyu kenan, Mataimakin gwamnan ya fito ya musanta jita-jitar cewa yana shirin sauya sheka zuwa tsohuwar jam'iyyarsa APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa ya ce:

"A karan kai na Philips Shaibu ba na shirin barin jam'iyya yanzu. Amma a gare ni, masoya na da masoyan gwamna Obaseki, waɗan da suka bar APC zuwa PDP, duk suna shirin barin PDP, amma ban san inda suka dosa ba."
"Muna ganin kamar ba'a amince da mu a PDP ba, kuma wannan dalilin yasa muke tunanin ya dace mu yarda kwallon mangwaro mu huta da kuda."
"Maganar gaskiya gwamna na cigaba da kokari duba da taron mu na jiya. Wasun mu ba su ji daɗin kalaman gwamna ba na cewa ba zai fita PDP ba.

Kara karanta wannan

Babu wani aibu don mutum ya sauya sheka a siyasa - Kwankwaso

Meke faruwa a siyasar Edo?

Mataimakin gwamnan ya tsage gaskiya, ya ce da yawa sun fice daga APC ne ba wai domin suna kaunar komawa PDP ba, kamar yadda Punch ta rahoto.

A cewarsa, sun bar APC ne saboda karan tsana da shugaban jam'iyyar na ƙasa ya dora wa gwamna Obaseki na Edo a wancan lokacin.

A wani labarin kuma Kwamitin tsarin karba-karba ya mika rahoto ga sabon shugaban APC

Gwamnan Jihar Kwara ya miƙa rahoton kwamitinsa na tsarin raba mukamai ga shugaban rikon kwarya na APC ta kasa.

Rahoto ya nuna cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, shugaban kwamitin ne ya mika rahoton ga gwamna Bello.

Asali: Legit.ng

Online view pixel