Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo

Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo

  • Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa kamata yayi ace wasu daga cikin mutanen da ke neman shugaban Najeriya a 2023 suna a gidan yari
  • Tsohon shugaban kasar ya ce da ace hukumar EFCC na aikinta yadda ya kamata toh da ya ci ace an daure su
  • Obasanjo ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na bikin cikarsa shekaru 85 a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun

Ogun - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Asabar, 5 ga watan Maris, ya ce da ace hukumar EFCC na aikinta yadda ya kamata toh da ya kamata ace wasu masu neman takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a 2023 suna a gidan yari.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na bikin cikarsa shekaru 85 a Abeokuta, babban birninjihar Ogun, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam

Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo
Obasanjo ya yi hannunka mai sanda ga wasu masu neman takarar shugaban kasa Hoto: : Femi Adesina
Asali: Depositphotos

Bana goyon bayan kowani dan takara - Obasanjo

Tsohon shugaban kasar ya ce koda dai masu neman takarar shugaban kasa da dama sun ziyarce shi domin neman goyon bayansa, shi bai tsayar da wani dan takara da zai marawa baya ba.

Ya ce:

“Bana daukar nauyin kowani dan takara daga kudu. Yayin da masu neman takara ke ta gwagwarmaya a kokarinsu na zama wanda ke rike da tutar jam’iyya na babbar kujerar kasar, na karanta kuma na ji batun goyon baya da jawaban goyon yan takara wanda a zahirin gaskiya ban yi su ba da kuma kafa jam’iyyun siyasa da ba zan taba kasancewa a ciki ba. An fada mani cewa soshiyal midiya ya alakantani da ambatan sunayen mutane uku daga kudu cewa ina daukar nauyin takarar shugabancinsu a 2023."

Kara karanta wannan

Obasanjo: Galibin Masu Son Zama Shugaban Ƙasa Ya Kamata Suna Ɗaure a Gidan Yari

Da yake ci gaba da magana, ya ce kamata yayi ace wasu masu neman shugabancin 2023 suna a kurkuku da ace EFCC da sauran hukumomi masu alaka na aikinsu yadda ya kamata.

“Na kalli wasu daga cikin mutanen da ke yawo da kuma wadanda mutane ke yawo don su. Idan da EFCC da ICPC za su yi aikinsu yadda ya kamata da kuma samun goyon bayan bangaren shari’a, da yawancinsu suna gidan yari. Duk mutumin da ba shi da mutunci a kananan abubuwa ba zai iya samun mutunci manyan abubuwa ba.”

Ya kara da cewar ya zama dole a dauki hoton zuciyar masu neman takara da kyau sannan a ilimantar da yan Najeriya domin yin zabi nagari don ci gaban kasar, rahoton The Cable.

2023: Sarkin Katsina Ya Goyi Bayan Tinubu Ya Gaji Kujerar Buhari

A wani labarin, Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, ya nuna goyon bayansa ga takarar Sanata Ahmed Bola Tinubu na shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Saraki: Yadda kura-kuran PDP ya kawo Buhari kan karagar mulki

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tarbar wata tawagar kungiyoyin Arewa masu goyon bayan takarar shugabancin kasar Tinubu da suka kai masa ziyara a fadarsa a ranar Juma'a a Katsina.

Sarkin ya ce Tinubu ya cancanta kuma zai shayar da ƴan Najeriya romon demokradiyya, rahoton Nigerian Tribune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel