2023: Sarkin Katsina Ya Goyi Bayan Tinubu Ya Gaji Kujerar Buhari

2023: Sarkin Katsina Ya Goyi Bayan Tinubu Ya Gaji Kujerar Buhari

  • Alhaji Abdulmumini Kabir, mai martaba sarkin Katsina ya nuna goyon bayansa ga takarar Sanata Bola Ahmed Tinubu
  • Sarkin ya ce Tinubu ya cancanta ya zama shugaban kasa domin ƙwarewarsa kuma zai shayar da yan Najeriya romon demokradiyya
  • Sarkin ya yi wannan jawabin ne a fadarsa da ke Katsina a ranar Juma'a yayin da tawagar kungiyoyin magoya bayan Tinubu

Jihar Katsina - Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, ya nuna goyon bayansa ga takarar Sanata Ahmed Bola Tinubu na shugabancin kasa.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tarbar wata tawagar kungiyoyin Arewa masu goyon bayan takarar shugabancin kasar Tinubu da suka kai masa ziyara a fadarsa a ranar Juma'a a Katsina.

2023: Sarkin Katsina Ya Goyi Bayan Tinubu Ya Gaji Kujerar Buhari
2023: Sarkin Katsina Ya Goyi Bayan Takarar Tinubu Na Shugabancin Kasa. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Muna Da Huja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu

Sarkin ya ce Tinubu ya cancanta kuma zai shayar da ƴan Najeriya romon demokradiyya, rahoton Nigerian Tribune.

A cewarsa, "Tinubu mutum ne da zai iya ceto yan Najeriya daga matsalolin tsaro, tattalin arziki da zamantakewar.
"Na san Tinubu tsawon shekaru saboda yana da kusanci da mahaifi na, Marigayi Sarkin Katsina, Alhaji Muhammad Kabir Usman."
"Muna ɗaukan Tinubu tamkar ɗan asalin Jihar Katsina ne saboda alaka mai tsawo da muke da shi.
"Muna goyon bayan sa ɗari bisa ɗari," in ji shi.

Sarkin ya yi kira ga sauran yan Najeriya su mara wa Tinubu baya saboda kwarewarsa.

Tunda farko, Shugaban tawagar, tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Abu Ibrahim ya shaidawa Sarkin cewa suna zagayawa ne domin neman hadin kan yan Najeriya su goyi bayan abokinsu da suke koyi da shi.

Abu Ibrahim ya yi alkawarin cewa Sanata Tinubu zai warware matsalolin Najeriya idan an zabe shi shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel