Dino Melaye ya dawo daga rakiyan Saraki, ya koma tafiyar Atiku

Dino Melaye ya dawo daga rakiyan Saraki, ya koma tafiyar Atiku

  • Gabannin babban zaben 2023, Sanata Dino Melaye ya magantu a kan wanda zai marawa baya domin ya zama shugaban kasa
  • Alamu sun nuna Melaye baya goyon bayan amininsa Bukola Saraki, domin an gano shi a wani taro da aka shirya na tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
  • Da yake magana a taron, tsohon sanatan ya yi hannunka mai sanda ga Saraki inda ya ce shi ya daina goyon bayan masu aniyar yin takara, cewa yan takara yake bi a yanzu

Abuja - Tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye ya watsar da Abubakar Bukola Saraki inda ya koma bayan Atiku Abubakar.

A wani bidiyo da ke yawo, Melaye ya yi magana a wani taro da ya gudana tsakanin Atiku da wasu sanatoci a Abuja, inda ya bayyana dalilin da yasa yake bayan Atiku, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Duk za mu mutu: Yaro ya fashe da kuka, yana tsoron ka da Rasha ta harbo bam Najeriya

Dino Melaye ya dawo daga rakiyan Saraki, ya koma tafiyar Atiku
Dino Melaye ya dawo daga rakiyan Saraki, ya koma tafiyar Atiku Hoto: PM News
Asali: Facebook

Dino ya ce wasu takwarorinsa a majalisar dattawa suna ta al’ajabin dalilin da yasa yake bin Atiku alhalin tsohon ubangidansa na majalisar dattawa wato Saraki shima ya nuna sha'awarsa ga takarar kujerar shugaban kasa.

Daga nan sai ya yi abin da ya ba da mamaki, wato ya yi watsi da kudirin takarar shugabancin Saraki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana a gaban jama'ar da suka halarci taron ciki harda Atiku, Dino ya ce:

“Wasu takwarorina sun ce dani Dino ya haka? Ya muka ganka a nan mun zata a wani wajen ya kamata mu ganka, sai na ce masu na daina bin masu aniyar yin takara. Yanzu yan takara nake bi. Bana so na gwada duk wani mutum da bai taba zama dan takara ba.”

Bayan ya fadi haka, sai mutanen da ke wajen suka dara tare da jinjina masa.

Kara karanta wannan

Atiku ya raina ‘yan PDP, ya dauka za su ba shi takara, za a sha mamaki a 2023 inji Wike

Kalli bidiyon wanda wani dan kashenin Atiku, Mohammed Abubakar, ya wallafa a shafinsa na Twitter:

Akwai kusanci sosai tsakanin Saraki da Dino

Melaye da Saraki sun kasance abokai na kut-da-kut a baya musamman a bangaren siyasa. A tare suka koma APC a 2014 sannan kuma suka barta zuwa PDP a shekarar 2018.

Saraki da Dino basu samu komawa kujerunsu ba bayan yan takarar APC sun lallasa su a zaben da ya gabata.

Zaben 2023 damar karshe ce ga Najeriya – Atiku ya shiga neman tikitin PDP gadan-gadan

A wani labarin, tohon ‘dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kuma jaddada niyyarsa na neman mulkin Najeriya, inda ya ce burinsa kawo gyara a kasar nan.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa Atiku Abubakar ya gana da wasu ‘yan jam’iyyar PDP da ke majalisar tarayya, ya na neman goyon bayansu a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ba abin yarda ba ne: Kul PDP ta amince da Atiku a 2023 - Tsohon Mai magana da yawunsa

Wazirin na Adamawa, Atiku Abubakar, ya gargadi al’umma a kan zaben ‘yan takara na gari a 2023, ya ce idan aka yi zaben tumun-dare, lallai an shiga uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel