Atiku ya raina ‘yan PDP, ya dauka za su ba shi takara, za a sha mamaki a 2023 inji Wike

Atiku ya raina ‘yan PDP, ya dauka za su ba shi takara, za a sha mamaki a 2023 inji Wike

  • Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya maida martani kan wasu kalamai da aka ji Atiku Abubakar ya yi
  • Nyesom Wike ya yi magana ne bayan Atiku ya ci-baki da cewa ba ya rasa samun takara a jam'iyya
  • Wike ya fadawa Atiku ya iya bakinsa, ya kuma nuna za ayi mamakin abin da za a gani a zaben 2023

Rivers – Mai girma Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi martani a kan kalaman da Atiku Abubakar ya yi a game da samun tikiti a jam’iyyar PDP.

Jaridar Vanguard ta rahoto Nyesom Wike yana yi wa Atiku Abubakar kaca-kaca, ya ce maganar da ya yi, ya nuna ya raina masu tsaida ‘dan takara a PDP.

Gwamnan ya fitar da jawabi a Fatakwal, jihar Ribas inda ya ce sakamakon zaben fitar da gwanin da za a gani a jam’iyyar adawa ta PDP zai ba mutane mamaki.

Kara karanta wannan

Ba abin yarda ba ne: Kul PDP ta amince da Atiku a 2023 - Tsohon Mai magana da yawunsa

Nyesom Wike ya kara da cewa sauran ‘yan takara za su marawa wanda ya samu nasara a 2023.

Da yake magana da bakin Mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri, ya ce Atiku ya wuce gona da iri da kalaman da aka ji daga bakinsa.

Atiku da Wike
Atiku Abubakar da Gwamna Wike Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Jawabin Hadimin Wike

Gwamnan ya yi kira ga ‘ya ‘yan babbar jam’iyyar hamayyar kasar da su iya bakinsu, su daina sakin kalaman da za su iya jawo rabuwar kan al’umma.

“Ban yi tunanin jin Atiku yana fadar wannan magana ba, cewa a ko yaushe yana samun tikitin PDP ya yi nisa, ya na nufin raina masu tsaida ‘dan takara.”
“Mutane su zura idanu, idan har zaben tsaida ‘dan takarar jam’iyyar PDP ake yi, sakamakon zai girgiza mutane. Jama’a su sa ido su ga abin da zai faru.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya ajiye siyasa, ya ba Buhari shawara a kan rikicin Rasha v Ukraine

“Wasu su na son raina wasu mutanen, kuma yin hakan bai dace a siyasa ba.” - Kelvin Ebiri.

Shirin 2023

The Cable ta ce Wike ya kuma tofa albarkacin bakinsa a game da jadawalin zaben 2023 da INEC ta fitar, ya ce yana sa ran 'Yan PDP-NWC za su yi aiki da lokaci.

Gwamnan ya kuma yabawa shugabannin jam’iyyarsu ta PDP a game da nasarorin da suka samu a zaben da aka gudanar a Filato, Kuros Riba da kuma jihar Ondo.

A rabu da Atiku - Kassim Afegbua

Ku na da labari cewa yunkurin takarar Atiku Abubakar na fuskantar barazana, ‘Dan Jam’iyya ya fito ya yi masa kaca-kaca a fili, ya bada shawarar PDP ta guje masa.

Kassim Afegbua ya ce mutumin da ya na fadi zabe a hannun Buhari, ya tsere Dubai ya bar su da APC watau Atiku Abubakar bai dace ya samu tikitin PDP a 2023 ba.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

Asali: Legit.ng

Online view pixel