Zaben 2023 damar karshe ce ga Najeriya – Atiku ya shiga neman tikitin PDP gadan-gadan

Zaben 2023 damar karshe ce ga Najeriya – Atiku ya shiga neman tikitin PDP gadan-gadan

  • Alhaji Atiku Abubakar ya hadu da ‘yan PDP a majalisa a game da batun takarar shugaban kasa a 2023
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar yana neman goyon bayan ‘yan majalisa wajen samun takara
  • Atiku yana ganin ya cancanci ya rike Najeriya, ya ce za a shiga matsala idan aka zabi tumun-dare

Abuja - Tsohon ‘dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kuma jaddada niyyarsa na neman mulkin Najeriya, inda ya ce burinsa kawo gyara a kasar nan.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa Atiku Abubakar ya gana da wasu ‘yan jam’iyyar PDP da ke majalisar tarayya, ya na neman goyon bayansu a zaben 2023.

Wazirin na Adamawa, Atiku Abubakar, ya gargadi al’umma a kan zaben ‘yan takara na gari a 2023, ya ce idan aka yi zaben tumun-dare, lallai an shiga uku.

Kara karanta wannan

Atiku ya raina ‘yan PDP, ya dauka za su ba shi takara, za a sha mamaki a 2023 inji Wike

‘Dan siyasar ya hadu da ‘yan majalisar ne saboda ya san irin rawar da za su iya takawa a jam’iyya, ya ce don haka ne ya fara yunkurin neman takara daga gare su.

"Na san tasirinku a PDP"

“Na san irin karfinku a jam’iyyarmu, kuma ina girmama maku sosai. Shiyasa na zabe ku a matsayin jerin wadanda zan fara haduwa da su a kan batun takarar shugaban kasar Najeriya a 2023.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku
Atiku ya na kamfe a Benuwai Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

“Saboda haka, ina mai mika maku kai na, ina neman goyon bayan ku wajen samun takara a PDP.”
“Na yi aiki a mataki na sama da na kasa. A matsayin mataimakin shugaban kasa, na kawo tsare-tsare na cigaba da suka kawo gyara da sauyi a dokar kasa.”
“A matsayin ‘dan kasuwa, na magance matsalolin al’umma, na ba dubunnan mutane aiki.”

Kara karanta wannan

Siyasar 2023: Atiku, Tinubu da sauran ‘Yan takara za su san matsayarsu nan da kwana 92

Ana neman mu dawo mulki - Atiku

A wani rahoto da ya fito daga shafin Reuben Abati, an ji ‘dan takarar shugaban kasa yana cewa a wannan karon, al’ummar Najeriya su na bukatarsu ido da rufe.

Atiku ya ce ana bukatar shugaban da ya san kan aiki, wanda zai iya hada-kan al’umma. Waziri ya shaidawa ‘yan majalisa cewa ya cika duka wadannan sharuda.

An yi wannan zama tsakanin Atiku da ‘yan majalisar ne a gidan Hon. Ndudi Elumelu a Wuse II, Abuja. ‘Yan majalisa da-dama sun samu halartar wannan zaman.

Yadda za a ci zabe - Tambuwal

A makon nan ne Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya fadi wasu hanyoyin da PDP za ta bi domin ta iya tika jam’iyyar APC mai mulki da kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Gwamnan na Sokoto yana cewa mutanen kasar nan sun yafewa Buhari laifin da ya yi a 1984, ya ce abin da ya rage masa shi ne ya shirya zabe na gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya ajiye siyasa, ya ba Buhari shawara a kan rikicin Rasha v Ukraine

Asali: Legit.ng

Online view pixel